Bahaushe tun asali ba cima-zaune ba ne, yana da sana’o’i domin samar da abinci, sutura, muhalli da dogaro da kai. Sana’o’in Bahaushe na da rassa huxu; noma (yawaituwa), kasuwanci (sayarwa), aiwatarwa (skills) da sana’o’in bixa.
Yahaya da wasu (1992) sun raba sana’o’i gida uku, a kasan kowanne ya samar musu ‘ya’ya, a qasan noma, akwai qira, saqa, dukanci. A kasuwanci, akwai dillanci da fatauci da sauransu. Kaso na uku su ne, qunshi, soye-soye, gyare-gyare, gashe gashe.
Noma, shi ne xaxxanar sana’ar Bahaushe ce da ma mutanen duniya baki xaya (Alhassan da wasu 1982), sai farautar dabbobin daji da harbin tsuntsaye. Bahaushe na fatauci, kasuwanci, su (kamun kifi), shiqa, farauta, harbi, gini, sassaka, jima, qira, gini, saqa, dukkanci, rini, wamzanci, fawa, sarrafa abinci (shiqa, daka, niqa, dafe dafe, soye-soye da gashe-gashe).
Domin karanta bayani akan Addinin Bahaushe Danna nan
Wani abu game da sana’o’in Hausawa, a da, mutum yana gadon sana’ar gidansu ne (xan gado), wanda kuma ya kama sana’ar da ba ta gidansu ba, ana ce ma ‘shaye’(shigege) (Niang, 2005). Misali, a garin Haxejia, akwai unguwannin masu sana’o’i, kamar unguwar Masaqa, inda ake saqa; akwai Unguwar dukawa, Majema, Maqera, unguwar Sarkin Ruwa, Unguwar Sanqira da sauransu.
Yadda Bahaushe ke koyon sana’a kuma, ana koyo ne a barance, saboda babu rubutu. Idan yaro ya kai shekara bakwai (7) da haihuwa, bayan an yi masa shayi, za a kai shi yana kallo yadda ake yin sana’a. Daga shekara sha uku (13) za a fara sa shi qananan aiyuka. Daga shekara sha takwas (18) zai fara manyan aiyuka, shekara 20 kuma za a barin sa yana aiyuka, ko ba dubawa, shekara 25 – 27, za a ‘yanta shi.