Yadda Ake Sabulun Wanka Da Wanki

0
71

A yau za mu kawo muku yadda ake yin sabulun wanki da wanka. Sabulun wanki da wanka yana cire dauɗar jiki da na tufafi. Wannan sabulun za ki iya siyar wa ko kuma ki yi amfani da shi a gida, kin ga riba biyu kenan ki siyar sannan kuma ga amfanin gida, kin huta siya tun da ke ma mai haɗawa ce.

Sannan za ki ga kin samu sauƙin siyan sabulu, tun da kin iya haɗawa kin ga mai gida ya huta siya, kin ga kin rage masa wani nauyin ga kuma tsaftar jikinki da ta tufafi.

GARGAƊI

1.  A kiyaye yin sa gaban yara, saboda kwastik soda [costic soda] tana da hatsari sosai, mu kiyaye lafiyar jiki da hannu wajen gujewa haɗarin chemical na kwastik soda.

2.  A kiyaye zuba kwastik soda[costic soda][ fiye da ƙa’ida, saboda yin hakan babban haɗarari ne ga lafiyar jiki da tufafi.

3.  A tabbatar da an gane haɗin wannan sabulun, idan ba ka gane ba ka nemi ƙarin bayani a wajenmu.

4- Ya zama ba bu kuskure wajen siyan kayan.

SINADARAN DA AKE BUƘATA

1-Kwastik soda [Costic soda] 1kg

2- P.K.O oil   6 littres

3- Ruwa 4kg

SAI KUMA

Sikeli [ma’auni]

Muciya

YADDA AKE HAƊAWA

Da farko za ki fara zuba kwastik soda [costic soda] a babban mazubi 1kg, sannan sai ki ɗebo ruwa 4kg, sai ki fara zuba kwastic soda ɗinki a cikin wannan ruwan da ki ka auna, sai ki fara juya shi da muciya a hankali.

Yayin da ki ke juyawa za ki ga yana hayaƙi sai ki bar shi ya yi kamar minti shida, bayan ya huce sai ki zuba ruwan PKO oil ɗin ki  a ciki kina zubawa kina juyawa har ya haɗe jikinsa.

Dama kin tanadi tukunyarki mai ɗan faɗi, sai ki sanya ledar sukari a ciki mai faɗi ita ma, sai ki juye wannan haɗin sabulun a ciki. Shikkenan kin gama sabulunki.

Sai ki bar shi ya bushe zuwa kamar awa uku ko biyu lokacin ya bushe sai ki cire shi a cikin ledar ki yanka shi yadda ki ke so. Idan kuma kina son ya yi miki mai shakali (shape) mai kyau sai ki siyo abin zuba sabulu, wajen ma su siyar da kayan kek (cake).

Za ki gan shi kamar roba-roba. Yana da shakali na triangle akwai mai circle. Sai ki ga ya fito da shakali mai kyau.

Shikkenan mun kammala sabulunmu. Sannan idan mutum yana buƙata zai iya sanya kalar da yake so, ko kuma sanya sinadarin ƙamshin da ki ke buƙata domin ya ba da ƙamshi na musamman.

Domin karanta yadda ake haɗa sabulu na ruwa na wanki ko sabulun wanki ko na wanka, ko yadda ake haɗa man gashi danna nan Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta wannan lambar 07068606171

Ko kuma ka je kai tsaye cikin tasharmu ta Youtube domin kallon yadda ake haɗawa cikin sauƙi, mai suna WikiHausa

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

 

 

 

 

 

 

labarin da ya wuceTarihin Ranar Damokuraɗiyya A Najeriya
Labarin na GabaMa’anar Damokuraɗiyya