Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙwanƙwamai - Tana nufin mugayen aljanu ko iskokai. Misali: A tatsuniyar da kakarsu ta ba su, ta ambaci wasu ƙwanƙwamai da ke zaune a cikin daji. ENG: Evil Spirit (A turance tana nufin ƙwanƙwamai)
Ƙwanƙwasa - Tana nufin bugun ƙofa, bango, ko wani abu da hannu. Misali: Ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan kafin ya shiga. ENG: Knock (A turance tana nufin ƙwanƙwasa)
Ƙwara - Tana nufin yaudara, cuta, ko samun wani abu ta hanyar rashin gaskiya ko dabara mara kyau. Misali: Idan aka ba ni dubu biyu a cikin kuɗinan ni aka ƙwara saboda na fi kowa yin aikin. ENG: Cheat (A turance tana nufin ƙwara)
Ƙwarai - Tana nufin sosai, ana amfani da ita wajen ƙarfafa ma’ana. Misali: Na gode ƙwarai da taimakon da ka ba ni. ENG: Very Much (A turance tana nufin ƙwarai)
Ƙwarangwal - Tana nufin ƙasusuwan jiki gaba ɗaya da suke ba jiki tsari, ƙarfi, da kariya ga gabobin ciki. Misali: Masana kimiyya sun gano ƙwarangwal ɗin wata tsohuwar dabba a ƙarƙashin ƙasa. ENG: Skeleton (A turance tana nufin ƙwarangwal)
Ƙwarbai - Tana nufin wahala, tsanani, ko yanayi mai wuya da ke kawo cikas wajen yin wani abu. Misali: Ya fuskanci ƙwarbai sosai kafin ya kammala karatunsa. ENG: Difficulty (A turance tana nufin ƙwarbai)
Ƙware - Tana nufin samun cikakkiyar gogewa a wani fanni sakamakon koyo, horo, ko yawan aiki a kansa. Misali: Bayan shekaru da dama yana aikin kafinta, ya ƙware sosai a sana’ar. ENG: Become Expert (A turance tana nufin ƙware)
Ƙware - Tana nufin shaƙewa ko toshewar maƙogwaro ta yadda numfashi ko haɗiyar abinci zai yi wuya. Misali: Yaron ya ƙware da abinci. ENG: Choke (A turance tana nufin ƙware)
Ƙwaƙule - Tana nufin fito da wani abu daga cikin wani abu ta hanyar hako, ko ƙwakkwafe shi daga ciki. Misali: Dodannin na ƙwaƙule idanun dabbobin da suka kama. ENG: Scrape Out from Inside (A turance tana nufin ƙwaƙule)
Ƙwaƙwa - Tana nufin yawan yin tambayoyi, son sani, ko binciken abubuwa domin samun ƙarin bayani da fahimta. Misali: Yaron yana da ƙwaƙwa sosai, domin kullum yana tambayar abubuwan da yake ji da gani. ENG: Being Inquisitive (A turance tana nufin ƙwaƙwa)
1 345 346 347 348