Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙurmus - Tana nufin ƙonewa gaba ɗaya har abu ya lalace ko ya zama toka.
Misali: Wutar ta ƙona gidan ƙurmus cikin ɗan lokaci kaɗan.
ENG: Burn Completely (A turance tana nufin ƙurmus)
Ƙuru - Tana nufin ɗaukar haɗari ko shiga wani al’amari ba tare da cikakken tabbaci ba.
Misali: Ya yi ƙuru wajen zuba duk kuɗinsa a sabon kasuwancin ba tare da bincike ba.
ENG: Taking a Risk (A turance tana nufin ƙuru)
Ƙuruciya - Tana nufin lokacin yarinta wato lokacin da mutum yake yaro.
Misali: A lokacin ƙuruciyarsa, ya kasance mai himma wajen karatu da wasanni.
ENG: Youthfulness (A turance tana nufin ƙuruciya)
Ƙurungu - Ƙurungu wani nau’in kifi ne mai gemu da tabo a jikinsa, wanda ake samu a kogi da tafki.
Misali: Masunci ya kama ƙurungu a kogi yau da safe.
ENG: Spotted Catfish (A turance tana nufin ƙurungu)
Ƙusa - Tana nufin wani nau'in ƙarfe mai tsini daga ƙarshensa wanda ake amfan da shi wajen haɗe katako ko a buga a bango don rataye abu.
Misali: Kafintan ya buga ƙusa a jikin bencin da ya karye.
ENG: Nail (A turance tana nufin ƙusa)
Ƙusumbi - Tana nufin tudun nama da yake bayan mutum ko wasu dabbobi kamar raƙumi da sauransu.
Misali: Raƙumi yana da ƙusumbi a bayansa wanda yake adana kitse.
ENG: Hump (A turance tana nufin ƙusumbi)
Ƙuƙuta - Tana nufin yin iya bakin ƙoƙari ko dagewa sosai domin cimma wani buri ko kammala wani aiki.
Misali: Ya ƙuƙuta matuƙa wajen neman ilimi har ya samu nasara.
ENG: Try Hard (A turance tana nufin ƙuƙuta)
Ƙwace - Tana nufin karɓe abu daga hannun wani da ƙarfi ko ba tare da izininsa ba.
Misali: Ɓarayin sun ƙwace wayarsa a kan hanya da dare.
ENG: Take by Force (A turance tana nufin ƙwace)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwafa - Tana nufin yin wani sauti daga makogwaro ko harshe domin nuna fushi, ɓacin rai, ko rashin jin daɗi.
Misali: Da ya ji abin da aka faɗa masa, sai ya yi ƙwafa ya juya ba tare da ya ce komai ba.
ENG: Clicking sound made in the throat to indicate anger (A turance tana nufin ƙwafa)