Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙuƙuta - Tana nufin yin iya bakin ƙoƙari ko dagewa sosai domin cimma wani buri ko kammala wani aiki. Misali: Ya ƙuƙuta matuƙa wajen neman ilimi har ya samu nasara. ENG: Try Hard (A turance tana nufin ƙuƙuta)
Ƙwace - Tana nufin karɓe abu daga hannun wani da ƙarfi ko ba tare da izininsa ba. Misali: Ɓarayin sun ƙwace wayarsa a kan hanya da dare. ENG: Take by Force (A turance tana nufin ƙwace)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwafa - Tana nufin yin wani sauti daga makogwaro ko harshe domin nuna fushi, ɓacin rai, ko rashin jin daɗi. Misali: Da ya ji abin da aka faɗa masa, sai ya yi ƙwafa ya juya ba tare da ya ce komai ba. ENG: Clicking sound made in the throat to indicate anger (A turance tana nufin ƙwafa)
Ƙwai - Tana nufin abin da tsuntsaye da wasu dabbobi ke yi wanda ke ɗauke da ɗa, kuma ana amfani da shi a matsayin abinci. Dabbobin da tsuntsayen kan yi ƙwai a madadin haihuwa. Misali: Ta dafa ƙwai biyu domin karin kumallo. ENG: Egg (A turance tana nufin ƙwai)
Ƙwainanuwa - Tana nufin yarinya mai hankali, basira, da fahimta fiye da yadda ake tsammani a shekarunta. Misali: Aisha ƙwainanuwa ce, domin tana yin magana da hikima da tunani duk da ƙanƙantar shekarunta. ENG: Wise Young Girl (A turance tana nufin ƙwainanuwa)
Ƙwala - Tana nufin yin kira da ƙarfi ko bugawa mutum wani abu. Misali: Sun dawo bayan Ibrahim ya ƙwala musu kira. ENG: Resound (A turance tana nufin ƙwala)
Ƙwallo - Tana nufin abu mai zagayayyiyar siffa da ake amfani da shi wajen wasanni, musamman ƙwallon ƙafa, ƙwallon kwando, da makamantansu. Misali: Yara suna buga ƙwallo a filin wasa bayan makaranta. ENG: Ball (A turance tana nufin ƙwallo)
Ƙwambo - Tana nufin taƙama, nuna isa, ko yawaita yabon kai da abin da mutum yake da shi ko ya aikata. Misali: Ya fito yana ƙwambo saboda ya saka sababbin kaya. ENG: Boastfulness (A turance tana nufin ƙwambo)
Ƙwanso - Tana nufin ƙwarya ko ɓawon da ke rufe iri ko ‘ya’yan wasu tsirrai, kamar wake, gyaɗa, ko makamantansu. Misali: Yara suna cire wake daga cikin ƙwansonsa kafin a dafa shi. ENG: Pod / Shell (A turance tana nufin ƙwanso)
1 344 345 346 347 348