Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙura - Tana nufin ɓarɓashin ƙasa da ke tashi a iska ko taruwa a saman abubuwa. Misali: Iska mai ƙarfi ta tayar da ƙura a kan hanya. ENG: Dust (A turance tana nufin ƙura).
Ƙurewa - Tana nufin iyaka ko ƙarshen wani abu, ko kuma matsayi mafi ƙololuwa da za a iya kaiwa. Misali: Ta ajiye kayanta ƙurewar ɗakinsu. ENG: Extremity (A turance tana nufin ƙurewa)
Ƙuri’a - Tana nufin zaɓi, ko ra'ayin mutum. Misali: 'Yan ƙasa sun fito domin kaɗa ƙuri'arsu a ranar zaɓe. ENG: Vote (A turance tana nufin ƙuri'a)
Ƙurji - Tana nufin ƙarami ko babban kumburi da ke fitowa a fata, wanda galibi ke ɗauke da ruwa ko mugunya. Misali: Wani ƙurji ya fito masa a fuska, wanda ya sa gurin ya kumbura. ENG: Pimple / Boil (A turance tana nufin ƙurji)
Ƙurmus - Tana nufin ƙonewa gaba ɗaya har abu ya lalace ko ya zama toka. Misali: Wutar ta ƙona gidan ƙurmus cikin ɗan lokaci kaɗan. ENG: Burn Completely (A turance tana nufin ƙurmus)
Ƙuru - Tana nufin ɗaukar haɗari ko shiga wani al’amari ba tare da cikakken tabbaci ba. Misali: Ya yi ƙuru wajen zuba duk kuɗinsa a sabon kasuwancin ba tare da bincike ba. ENG: Taking a Risk (A turance tana nufin ƙuru)
Ƙuruciya - Tana nufin lokacin yarinta wato lokacin da mutum yake yaro. Misali: A lokacin ƙuruciyarsa, ya kasance mai himma wajen karatu da wasanni. ENG: Youthfulness (A turance tana nufin ƙuruciya)
Ƙurungu - Ƙurungu wani nau’in kifi ne mai gemu da tabo a jikinsa, wanda ake samu a kogi da tafki. Misali: Masunci ya kama ƙurungu a kogi yau da safe. ENG: Spotted Catfish (A turance tana nufin ƙurungu)
Ƙusa - Tana nufin wani nau'in ƙarfe mai tsini daga ƙarshensa wanda ake amfan da shi wajen haɗe katako ko a buga a bango don rataye abu. Misali: Kafintan ya buga ƙusa a jikin bencin da ya karye. ENG: Nail (A turance tana nufin ƙusa)
Ƙuƙuta - Tana nufin yin iya bakin ƙoƙari ko dagewa sosai domin cimma wani buri ko kammala wani aiki. Misali: Ya ƙuƙuta matuƙa wajen neman ilimi har ya samu nasara. ENG: Try Hard (A turance tana nufin ƙuƙuta)
1 341 342 343 344