Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙumbiya-ƙumbiya - Tana nufin yin magana ko bayani cikin karkacewa ba tare da zuwa kan ainihin batu kai tsaye ba.
Misali: Ka daina ƙumbiya-ƙumbiya ka faɗi abin da kake nufi kai tsaye.
ENG: Inability to come to the point; beating around the bush (A turance tana nufin ƙumbiya-ƙumbiya).
Ƙuna - Tana nufin tsananin zafi, musamman zafin rana, wuta, ko yanayi mai matuƙar zafi.
Misali: Yau rana ta yi matuƙar ƙuna da alama za a yi ruwan sama.
ENG: Great Heat (A turance tana nufin ƙuna)
Ƙunci - Tana nufin halin rashin jin daɗi ko zafin rai da mutum ke shiga.
Misali: Zuciya na ƙunci idan ta rasa makusancinta.
ENG: Bad Temper (A turance tana nufin ƙunci).
Ƙundu - Tana nufin wani ɓangare na cikin tsuntsaye, musamman kaji, wanda ke taimakawa wajen niƙa abinci kafin ya ci gaba da narkewa.
Misali: Wasu mutane suna son cin ƙundu idan aka dafa kaza.
ENG: Gizzard (A turance tana nufin ƙundu)
Ƙungiya - Tana nufin taron mutane da suka haɗu domin wata manufa guda, aiki, ko amfani na bai ɗaya.
Misali: Ya shiga ƙungiyar matasa domin ya ba da gudummawa wajen cigaban al'umma.
ENG: Society / Union (A turance tana nufin ƙungiya)
Ƙungurmi - Tana nufin tsanani ko tantagarya.
Misali: Sun shiga cikin ƙungurmin daji domin yin farauta.
ENG: Bare State (A turance tana nufin ƙungurmi).
Ƙunsa - Tana nufin kasancewar wani abu a cikin wani abu.
Misali: Wannan littafin tarihin Hausawa ya ƙunsa.
ENG: Contain (A turance tana nufin ƙunsa).
Ƙunshi - Tana nufin wani abu da aka naɗe ko aka shirya domin aikawa ko jigila zuwa wani wuri.
Misali: Na karɓi ƙunshi daga abokina wanda ke ɗauke da littattafai da kayan amfani.
ENG: Parcel (A turance tana nufin ƙunshi).
Ƙuntata - Tana nufin damu ko takura.
Misali: Yaron ya ci gaba da ƙuntata wa mahaifinsa da tambayoyi har sai da ya amsa masa.
ENG: Pester (A turance tana nufin ƙuntata)
Ƙura - Tana nufin kallon abu sosai ba tare da kau da ido ba.
Misali: Ta ƙura wa zanen ido saboda matuƙar kyawunsa.
ENG: Stare (A turance tana nufin ƙura)