Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

United Nations Industrial Development Organization (UNICEF) - Hukumar Bunƙasa Masana'antu Na Majilisar Ɗinkin Duniya
United Nations International Children’s Emergency Fund (UNICEF) - Hukumar Kyautata Rayuwar Yara Ta Majilisar Ɗinkin Duniya
United States Agency for International Development (USAID) - Hukumar Bunƙasa Ƙasashe Masu Tasowa Ta  Ƙasar Amurka
Universal Basic Education Commission (UBEC) - Hukumar llimin Baiɗaya
University - A turance tana nufin jami'a. Misali; Gambo ya shiga jami'a ne a shekarar da ta gabata. HAU; Jami'a (Tana nufin makarantar gaba da sakandire)
Unmaried person who was formally married - A turance tana nufin gwauro. Misali; Gwauro ne shi yanzu, ya saki matarsa a watan da ya gabata. HAU; Gwauro (Tana nufin wanda a halin yanzu ba shi da aure amma ya taɓa aure) Kishiyarta; Mai Aure
Untie - A turance tana nufin kwance. Misali; Ya kwance igiyar da aka ɗaure a jikin ƙofa. HAU; Kwance (Tana nufin warware abin da aka ɗaure ko sakin abu daga matsewa ko ƙulli)
Upper Benue River Basin Development Authority (UBRBDA) - Hukumar Bunƙasa Yankunan Kogin Binuwai
Upper storey of a house -

A turance tana nufin kwatashi.

Misali: Iyalan suna zaune a kwatashi yayin da shagunan suke ƙasan ginin.

HAU; Kwatashi (Tana nufin saman gida mai hawa-hawa, wato bene)

Uproot - A turance tana nufin ɓaɓɓake. Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa. HAU; Ɓaɓɓake (Tana nufin jijjige abu daga tushensa)
1 309 310 311 312 313 337