Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Uproot By Shaking - A turance tana nufin girgiɗe. Misali; An girgiɗe mata haƙorin don ya ishe ta da ciwo. HAU; Girgiɗe (Tana nufin cire abu da ƙarfi)
Urine - A turance yana nufin bawali. Misali; Ya yi bawali a ƙofar makaranta. HAU; Bawali (Tana nufin fitsari)
Urine - A turance tana nufin fitsari. Misali; Amir ya yi fitsari a jikinsa. HAU; Fitsari (Tana nufin wani ruwa da jiki ba ya buƙata wanda ke fitowa daga ƙoda)
Usefulness - A turance tana nufin fa'ida. Misali; Zumunci yana da fa'ida don yana sa albarka a rayuwa. HAU; Fa'ida (Tana nufin amfanin abu) Kishiyarta; Rashin Fa'ida
Using clever or deceitful means for some purpose - A turance tana nufin kissa. Misali; Ba asiri ta yi wajen fitar da abokiyar zamanta ba, kissa ce da kisisina. HAU; Kissa (Tana nufin yin amafani da wayo da dabara da hilata don cimma manufa)
Utterance - A turance tana nufin furuci. Misali; Yana da furuci daddaɗa. HAU; Furuci (Tana nufin yin magana)
Uwar Garke - Babbar ƙafa ko garken da yake ba wa sauran kafafen intanet damar shige da fice domin samun bayani.
Uwar Kudi - Jari ko tsagwaron kudin da ake juyawa a harkar kasuwanci.
Valley -

A turance tana nufin kwari.

Misali; Ruwa yana gudana a cikin kwari bayan damina.

HAU; Kwari (Tana nufin gangare ko ramin da ruwa ke taruwa ko ya wuce)

Variable-tone Drum - A turance tana nufin kalangu. Misali; 'Yan mata na son kiɗan kalangu matuƙa. HAU; Kalangu (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya)
1 310 311 312 313 314 337