Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Vein - A turance tana nufin jijiya. Misali; Allurar jijiya aka yi masa saboda zafin zazzaɓin. HAU; Jijiya (Tana nufin hanyar jini a jikin mutum ko dabba)
Verdict - A turance tana nufin hukunci. Misali; Duk wanda ya aikata laifi, za a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata. HAU; Hukunci (Tana nufin matsayi ko sakamakon abin da aka aikata ko za a aikata)
Very - A turance tana nufin ƙalau. Misali; Shanyin ya yi sanyi ƙalau sai an sake dafa shi. HAU; Ƙalau (Tana nufin sosai ko matuƙa)
Very heavy first rains of the rainy season -

A turance tana nufin kwazari. 

Misali: Kwazari ya sauka sosai a daren jiya har ya cika magudanan ruwa.

HAU; Kwazari (Tana nufin ruwan sama na farko mai ƙarfi a lokacin damina)

Very Short - A turance tana nufin ɗigil. Misali; Na ga wani ɗan ɗigil a kasuwa yau. HAU; Ɗigil (Tana nufin ɗan gajere ko ƙanƙani)
Very Sweet - A turance tana nufin carkwai. Misali; Raken yana da zaƙi carkwai. HAU; Carkwai (Tana nufin zaƙi sosai)
Very Wet - A turance tana nufin jagab. Misali; Ruwa ya jiƙa su jagab saboda ba su daɗe da fita ba ya sakko. HAU; Jagab (Tana nufin tsananin jiƙewa)
Veterinary Conucil of Nigeria (VCN) - Majalisar Likitocin Dabbobi Ta Najeriya
Vigilante Group of Nigeria (VGN) - Hukumar Jami'an Banga Ta Najeriya
Village -

A turance tana nufin ƙauye.

Misali: Habu ya tafi ziyara ƙauyen kakansa a ƙarshen mako.

HAU: Ƙauye (Tana nufin karkara ko inda ba birni ba)

1 311 312 313 314 315 337