Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tusk - A turance tana nufin haure.
Misali; Da hauren giwa ake haɗa maganin.
HAU; Haure (Tana nufin haƙori)
Twenty - A turance tana nufin ishirin.
Misali; Kaji guda ishirin ya siyo don gudanar da bikin.
HAU; Ishirin (Tana nufin goma sau biyu)
Twigs for firewood - A turance tana nufin ƙirare.
Misali: Yara sun je daji don samo tattara ƙirare.
HAU; Ƙirare (Tana nufin ƙananan rassan itace da ake tattarawa domin amfani da su wajen kunna wuta)
Two stringed, plucked musical instrument - A turance tana nufin garaya.
Misali; Gurin ya cika da masu kiɗan garaya don bikin na 'yan bori ne.
HAU; Garaya (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa na gargajiya)
Type of cloth without embroidery - A turance tana nufin gare.
Misali;Malam Audu ya sa gare.
HAU; Gare (Tana nufin rigar Hausawa mara ado)
Ulcerated Wound - A turance tana nufin gyambo.
Misali; Ai gyambon da ke ƙafarsa ya daɗe sosai.
HAU; Gyambo (Tana nufin ciwon da ba ya warkewa ko kuma ya daɗe bai warke ba)
Uncle - A turance tana nufin kawu.
Misali; A cikin mutanen da suka zo har da Kawu, shi ne ma ya jagoranci tafiyar.
HAU; Kawu (Tana nufin wa ko ƙanin mahaifi ko mahaifiya)
Uncompleted Building - A turance tana nufin kango.
Misali; Har yanzu ginin kango ne ba a ƙarasa ba.
HAU; Kango (Tana nufin ginin da ba a kammala ba)
Underneath - A turance tana nufin ƙarƙashi.
Misali; Katin ya faɗi a ƙarƙashin tebur.
HAU; Ƙarƙashi (Tana nufin abin da yake ƙasa).
Understand - A turance tana nufin gane.
Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi?
HAU; Gane (Tana nufin fahimta)
Kishiyarta; Rashin Ganewa