Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Tree - A turance tana nufin bishiya. Misali; Wannan itacen ɗorawa ne. HAU; Itace (Tana nufin bishiya)
Tribe -

A turance tana nufin ƙabila.

Misali; Hausa wata babbar ƙabila ce a Najeriya.

HAU; Ƙabila (Tana nufin rukunin mutane masu asali, al’ada da harshe iri ɗaya)

Tribunal - Kotun Wucin Gida
Tribunal Court - Kotun Wucin Gadi/Kotun Musamman
Truth - A turance tana nufin gaskiya. Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa. HAU; Gaskiya (Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi) Kishiyarta; Ƙarya
Try hard - A turance tana nufin ƙoƙarta. Misali: Ta ƙoƙarta sosai wajen kammala aikinta a kan lokaci. HAU: Ƙoƙarta (Tana nufin amfani da dukkan ƙarfi da himma wajen cimma wani abu)
Tsagaita - Tsahirtawa daga yin, ko barin wani abu ta hanyar taƙaitawa ko kaucewa, kamar daina yin abin da yake jawo ko haifar da asarar dukiya ko ta rayuwa.
Tsaron Sirri - Aikin tsaro ne da jami'an tsaro na farin kaya suke yi a boye domin nesa daga magauta.
Tuesday - A turance tana nufin rana ta biyu a mako. Misali; Kasuwar tana ci ranar Talata. HAU; Talata (Rana ta biyu a cikin ranakun mako)
Tunnel/Pipe - A turance tana nufin bututu. Misali; Mai gyaran bututun ya zo da wuri. HAU; Bututu (Tana nufin mazurari na ruwa ko iska da sauransu)
1 306 307 308 309 310 337