Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Showing eagerness - A turance tana nufin hanƙoro.
Misali; Tun safe yake hanƙoro, saboda za su buga ƙwallon ƙafa da abokansa.
HAU; Hanƙoro (Tana nufin nuna zaƙuwa)
Shrilling done by women to express joy - A turance tana nufin guɗa.
Misali; Matan sun kaure da guɗa a lokacin da aka shigo da amaryar.
HAU; Guɗa (Tana nufin wani salo na sarrafa ihu da mata ke yi musamman a lokutan farin ciki)
Side - A turance tana nufin gefe.
Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya.
HAU; Gefe (Tana nufin wani sashe)
Skilled - A turance tana nufin gogagge.
Misali; Ai malamin gogagge ne a fannin kimiyya da fasaha.
HAU; Gogagge (Tana nufin ƙwarewa a wani abu ko wani fanni)
Skin - A turance tana nufin fata.
Misali; Ana amfani da fata don yin jakunkuna da takalma.
HAU; Fata (Tana nufin abin da ya lulluɓe jikin mutum ko dabba)
Slave - A turance tana nufin bawa
Misali; Ya siyo bawa kuma yana ta azabtar da shi.
HAU; Bawa (Tana nufin Hadimi, ko mai yin hidima ga wani. Wanda kuma galibi siyansa ake yi)
Sleep - A turance tana nufin barci.
Misali; Da na je gidan na tarar yana barci, sai na koma.
HAU; Barci (Tana nufin rufe ido don hutawa ba tare da sanin abinda yake faruwa ba)
Small & Medium Enterprises Development Agency of Nigeria (SMEDAN) - Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana'antu Ta Najeriya
Small black biting ant - A turance tana nufin cinnaka.
Misali; Idan cinnaka ya ciji mutum gurin har ɗan kumbura yake.
HAU; Cinnaka (Tana nufin ɗan ƙaramin baƙin ƙwaro, yana cizo mai zafi)
Small patch or plot of land given to a young boy to farm on - A turance tana nufin gayauna.
Misali; An ba wa Ɗahiru gayauna saboda ya samu kuɗin hidimar bikin kalankuwa.
HAU; Gayauna (Tana nufin wani sashi na gona da ake ba wa matasa don su noma)