Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Speed/ Haste - A turance tana nufin hanzari.
Misali; Ku yi hanzari kar ku makara.
HAU; Hanzari (Tana nufin sauri ko gaggawa)
Spending Money In An Extravagant Way - A turance tana nufin bushasha.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake bushasha da kuɗin.
HAU; Bushasha (Tana nufin kashe kuɗi yanda aka ga dama musamman akan abubuwa marasa muhimmanci)
Spider - A turance tana nufin gizo.
Misali; Gizo-gizo ya yi yawa a ɗakin.
HAU; Gizo (Tana nufin ƙwaro mai yin yana a bango, yana da ƙafafu guda takwas)
Spinach - A turance yana nufin ganyen alayyahu.
Misali; Zan yi miyar alayyahu da yamma.
HAU; Alayyahu (Ganye ne mai ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya)
Spoil - A turance tana nufin dagula.
Misali; Yaran aji ɗaya sun dagula littattafansu.
HAU; Dagula (Tana nufin lalatawa)
Spoiled - A turance tana nufin ɓaci.
Misali; Rigar ta ɓaci da amai sai an sake wata.
HAU; Ɓaci (Tana nufin lalacewa)
Spoon - A turance tana nufin cibi.
Misali; A Sokoto cibi ake kiran cokali.
HAU; Cibi (Tana nufin cokali)
Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) - Ƙungiyar Marubuta Wasanni Ta Najeriya
Sprinkle - A turance tana nufin barbaɗa.
Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa.
HAU; Barbaɗa (Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba)
Squandering - A turance tana nufin facaka.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi.
HAU; Facaka (Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba)