Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Secret - A turance tana nufin asiri.
Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana satar kayan mutane.
HAU; Asiri (Tana nufin abinda yake a ɓoye)
Securities & Exchange Commission (SEC) - Hukumar Kadarori da Hada-hadar Hannun Jari
See something from afar - A turance tana nufin hanga.
Misali; Kamar Talatu na hanga tana shiga gidan maigari.
HAU; Hanga (Tana nufin gano abu daga nesa)
Senate of Nigeria - Majalisar Dattawan Najeriya
Senior Staff Association of Electrical & Allied Companies (SSAEAC) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Kamfanonin Kayan Lantarki
Senior Staff Association of Nigerian Polytechnics (SSANIP) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Makarantun Fasaha Ta Najeriya
Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya
Senior Staff Union of Colleges of Education in Nigeria (SSUCOEN) - Ƙungiyar Manyan Malaman Kwalejojin llimi Ta Najeriya
Sense - A turance tana nufin hankali.
Misali; Idris yana da hankali da sanin ya kamata.
HAU; Hankali (Tana nufin sanin ya kamata)
Kishiyarta: Rashin Hankali
September - A turance yana nufin wata na tara a shekara.
Misali; Sabon zangon karatuna farawa ne a watan Satumba.
HAU; Satumba (Wata ne na tara a shekara)