Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sermon - A turance tana nufin huɗuba.
Misali; Muna sauraron huɗuba daga masallaci mai alfarma a rediyo.
HAU; Huɗuba (Tana nufin jawabai na hikima da jan hankali don faɗakarwa ko kwaɗaitarwa a kan binn Allah da kuma gujewa saɓa masa)
Servant - A turance tana nufin bara.
Misali; Idris bara ne a gidan Alhaji Sani.
HAU; Bara (Tana nufin mai yin hidima a cikin gida)
Service - Hukuma, Ma'aikata
Serving God - A turance tana nufin ibada.
Misali; Idan mutum ya kasance mai ibada rayuwarsa tana albaraka.
HAU; Ibada (Tana nufin bautawa Allah)
Setting one person against another through gossip - A turance tana nufin gulma.
Misali; Musulunci ya haramta gulma.
HAU; Gulma (Tana nan nufin ɗaukar zancen wani a kai wa wani da zimmar haɗa su faɗa)
Sharpen - A turance tana nufin feƙe.
Misali; An feƙe wuƙaƙen kafin a yanka naman.
HAU; Feƙe (Tana nufin saka abu ya yi kaifi)
Shaving - A turance yana nufin kwashe gashi.
Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa.
HAU; Aski (Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban)
Shivering - A turance tana nufin ɓari.
Misali; Gambo sai ɓari yake saboda zafin zazzaɓi.
HAU; Ɓari (Tana nufin karkarwa saboda jin sanyi)
Short - A turance tana nufin guntu.
Misali; Da wani guntun itace na ƙarasa girkin.
HAU; Guntu (Tana nufin mara tsayi)
Kishiyarta; Dogo/ Mai tsayi
Short - A turance tana nufin gajere.
Misali; Na rubuta gajeren labari a shafin jaridar.
HAU: Gajere (Tana nufin mara tsayi)