Zakkar Fid-Da-Kai

0
357

Zakkar fid-da-kai sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), domin ya fitar kuma sahabban Sa masu albarka ma sun fitar. Shari’a ta shar’anta wannan zakka domin tsarkake masu azumi daga yasasshen zance da batsa; kuma ciyarwa ga miskinai inda za ta wadatar da su a ranar sallah ta farin ciki.

Hadisi daga Abdullahi Bn Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)ya farlanta zakkar fid-da-kai ta bayan Ramadan kan mutane” (Bukhari 3/291, Muslim 984). Haka zalika hadisin Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu), wanda Abu Dawud da Nasa’i suka fitar ya nuna hakan.

Hadisi ya tabbata daga Abu Sa’id Alkhudri (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Mun kasance muna bayar da ita a zamanin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) sa’i ɗaya daga abinci; ko sa’i ɗaya daga dabino, ko sa’i ɗaya daga alkama, ko sa’i ɗaya daga zabibi (busasshen inibi). A wata ruwayar “Sa’i ɗaya daga cikwi”. (Bukhari 1508, Muslim 985).

Ana fitar wa yaro, babba, mace, namiji da kuma bawa da ‘yantacce; saboda hadisin Abdullahi Bn Umar (Radiyallahu Anhu) da ya ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni a fitar wa yaro, babba, bawa da ‘yantaccen daga waɗanda kuke ɗaukar nauyinsu”.

(Darukuɗniy 2/141, Baihaƙiy 4/161).

Sannan ana bayar da ita ce kafin tafiya sallar idi, ba ya halarta a jinkirta ta har zuwa lokacin sallah; koda kwana ɗaya ko biyu kafin ranar sallah; ya halatta a fitar saboda abin da ya zo daga aikin Abdullahi Bn Umar (Radiyallahu Anhu).

Ya zo cikin hadisin Abdullahi Bn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa; “….. wanda duk ya bayar da ita kafin sallah, to ya yi ta karɓaɓɓiya; wanda kuma ya bayar bayan an yi sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki”.

Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal) danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijja danna nan.

Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceDaren Lailatul Ƙadari
Labarin na GabaSallar Asham Da Raka’o’inta