Yin Ƙarya Da Sunan Yarfen Siyasa.

0
969

Ƙarya na ɗaya daga cikin munanan ɗabi’un da ‘yan siyasa suke yi, wani abin da yake ƙara wa ƙaryar da suke yi muni shi ne, sauya mata suna da kiran ta YARFEN SIYASA.

Ya ‘yan ‘uwa musulmai! Ƙarya dai a Musulunce haramun ce, domin kuwa Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) ya ce : “….. na hana ku yin ƙarya, haƙiƙa, ƙarya tana kai mai Yin ta ga barin hanya madaidaiciya, barin hanya madaidaiciya kuma yana kai mutum wuta. Kuma mutum ba zai gushe ba, bayan ƙarya yana hasashen yin ƙaryar har sai ya kai ga an rubuta shi makaryaci a wajen Allah”.
Muslim ne ya rawaito shi
Sannan kuma an karɓo wani hadisin daga Samura Jundub, Allah ya yarda da shi cewa: “…. A wata safiya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Daren da ya gabata, wasu mala’iku biyu sun zo min a mafarki sai suka ce da ni: “Zo mu je……. Sai na tafi tare da su. Kwatsam sai ga mu …… a kan wani mutum da ke kwance a rigingine; sannan kuma ga wani tsaye a kansa ɗauke da lauje a daidai ɗaya daga ɓangarorin fuskarsa yana tsarge masa baki zuwa ƙeya, sannan sai ya koma ɗaya ɓangaren farko, kafin ya ƙare ɓangaren na biyu wancan ɓangaren na farko ya koma yadda yake (ya haɗe) sai ya sake komawa gare shi (don tsarge shi), sai ni kuma na ce: “Subhanallah wannan kuma me kenan?”. Sai aka ce min mutumin da ka ga ana tsargewa baki zuwa ƙeya, da hanci zuwa ƙeya, da ido zuwa ƙeya, wanda yake fita daga gidansa ne sai ya je ya shirga ƙarya da za ta yaɗu ta isa sassa daban-daban to haka za a yi ta yi masa har zuwa tashin kiyama.”
Bukhari ne ya rawaito shi
Ina masu zuwa kafafen yaɗa labarai su shirga ƙarya, ko kuma su ƙaryata tabbattacen abin da aka yi da sunan hamayyar siyasa, a yi hattara! Kuma su sani duk abin da ya fita daga bakunansu mala’iku na rubuta shi:
Ma’ana “Babu wata magana da (mutum) zai furta a wajensa akwai mala’ika mai tsaro halartacce.” (wato domin rubuta abin da ya furta). Ƙaaf, aya ta (18)
Sannan kuma ranar ƙiyama Allah zai yi musu hisabi a kai.

Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Hattara Dai ‘Yan Siyasar Musulmai wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin Danna nan.

labarin da ya wuceSaki-reshe Kama-ganyen Da ‘Yan Siyasa Suke Yi.
Labarin na GabaCin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa.