A lokacin da makaɗi ya zo yin waƙar baka tun a ƙwaƙwalwarsa da tunaninsa yake fara tsara ta. Wannan tsari shi ne na baɗini, wanda yake a rattaɓe a zuciyarsa kuma a cikin jumlolinsa.
To, tun daga wannan lokaci ne ya riga ya yi waƙarsa ta baka ta bin waɗannan matakai:
– Matakin Ƙullawa
– Matakin Kiɗa
– Matakin Rauji
– Matakin Kalmomi
– Gindin Waƙa
– Layuka ko Saɗaru a Ɗiya
-Nuna Farin Ciki
– Nuna Baƙin Ciki
-Faɗakarwa
-Gargaɗi
-Ilmantarwa
-Nasihantarwa
– Isharantarwa
-Yabawa
-Yin Zambo
-Yin Habaici
Da Sauransu Kamar Kalmomin Azancin Magana
Matakin Ƙullawa
Makaɗan baka sukan ƙulla waƙoƙinsu ta azanci da fasahar da suke da su.
Ma’anar ƙulli ta ƙamus:
A ƙamus na Hausa-English (Awde, 1996: 102) ya nuna Ƙulli shi ne (1) to knot (2)to plan (3) to conspire; wato (1)ya ƙulla (2) ya shirya ko ya yi dabara (3) ya haɗa kai. Shi kuma Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 285) cewa ya yi ƙulla, ita ce ɗaura ko ƙudura.
Ma’anar Ƙulli ko Ƙulla ko Ƙullawa ta isɗilahi wato ta fannin ilimin waƙar baka. Ita ce:
Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya faɗi yadda yake ƙulla waƙarsa a inda yake cewa:
Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,
‘Y/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,
Jagora: In naƙ ƙulla waƙa a ƙara man,
‘Y/Amshi: Mu haɗu duk azanci gare mu,
: Shin a a mutum guda za ya radde mu,
: Shirya kayan faɗa Maigida Tsahe,
: Ali ɗan Iro bai ɗauki reni ba.
(Ɗanƙwairo, Waƙar ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu II (1960-1991)
Ƙullawa ta waƙoƙin makaɗan baka tana da matakai biyu. Akwai ƙullawa ta makaɗan ƙungiya, sannan akwai ƙullawa ta makaɗan kaɗaita. Ga su kamar haka:
i) Ƙullawar Makaɗan Ƙungiya
Waƙoƙin baka na Hausa waɗanda ake ƙullawa ta ƙungiya, waƙoƙi ne waɗanda ake tunaninsu ta tsakanin Jagora da kuma ‘yan amshinsa. Ita ƙungiya ita ce wadda ta ƙunshi Jagora da kuma yaransa masu yi masa amshi na waƙar baka da kuma yin kiɗa.
Har wa yau, ƙungiya ta ƙunshi ‘yan ma’abba ko san-ƙirori ko masu kirarin baki. A wannan lokaci, za a haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin Jagora da ‘yan amshinsa, a dinga tunanin yadda za a shirya waƙa, musamman ta kawo jumloli da yadda za a tsara saɗaru ko layuka, sannan ana yi ana dakatawa ko lumfasawa. Wannan shi ne ƙulla waƙa ta makaɗan ƙungiya.
Su kuwa makaɗan kaɗaita, su ne waɗanda Jagororinsu kawai za su dinga ƙulla kalmomi da jumloli, amma yaransu, za a sami waɗanda suke yin amshi wato +ciko kawai, sai dai ba su yi musu kowane irin ƙari a waƙa. Akwai wasu jagororin da ba a ce musu ko ƙala, Jagora ne zai ƙulla waƙarsa kuma ya ƙare ta shi kaɗai. Irin wannan ƙulli jagora ne kawai zai yi tunanin waƙa a baɗininta idan ya gama ƙulla ta sai ya zo cikin yaransa ya rera ko ya je wani wuri ya sadar da ita. A irin wannan waƙa, Jagora ne kawai ake jin muryarsa yana rera waƙa, yana sadar da ita ga jama’a.
A bisa waɗannan matakai ne ake bi, ake ƙuƙƙulla, waƙoƙi na gargajiya ko waƙoƙi na zamani na baka da Hausawa suke yin tunaninsu a baɗini, daga baya su rera su a yayin da suke sadar da su.
Matakin Kiɗa
A Ƙamusun Hausa an nuna kiɗa yana nufin bugun ganga ko kalangu ko abun bugawa ko bugun ƙwarya ko goge ko garaya ko taushi ko kotso da hannu ko da makaɗi ko da wani abu (CNHN, 2006: 243).
A ilimin fannin waƙar baka, kiɗa yana nuni ne da wani amo ko sauti da ake samarwa ta gwama ko haɗa abubuwa biyu kamar dutsi + dutsi ko tafi + tafi ko baki + ƙahon dabbobi ko ganga + gula (makaɗi) ko wani abu + wani abu ko sauransu. Kiɗa kuma yakan zama wani amo ne wanda yakan shiga jikin mai sauraro, ya sa masa karsashi har ya dinga rausayawa, yana tattakawa ko jujjuyawa.
Gusau (2008: 54) yana ganin kiɗa shi ne wanzar da amo mai shiga jiki wanda kuma ake aiwatarwa ta haɗa abubuwa biyu ta matakin busawa ko tafawa ko bugawa ko kaɗawa ko gogawa ko girgizawa ko kuma wasun waɗannan.
Akwai kayayyakin kiɗa da dama. Wasu na gargajiyar Hausawa ne, wasu kuma na baƙin wasu al’ummu ne waɗanda Hausawan suka aro, suna amfani da su. A wajen Hausawa akwai kiɗa zallarsa kawai, ba tare da haɗawa da waƙa ba, ko kirari ko kaɗa take. Akwai kuma kiɗa ta amfani da kayan kiɗa wanda ake haɗawa da waƙa, wanda kuma ake yi wa waƙoƙin da makaɗan baka suke yi.
Kiɗa a wajen Hausawa ya rarrabu zuwa: Kiɗa
-waƙa +take -take +waƙa
-Waƙoƙin Gaɗa
-Waƙoƙin Samartaka
-Waƙoƙin Manyan Mata
-Waƙoƙin Manyan Maza
-Waƙoƙin Makaɗa
A wajen aiwatarwa ta waƙar baka akan gwama ta da amon kiɗa wanda za su dinga tafiya a tare tsakanin muryar makaɗi da sautin gangar da makaɗin yake amfani da ita. Bisa mahangar makaɗa, akwai wasu hanyoyi da ake ɗora kiɗa na waƙoƙinsu na baka domin su yi daidai da yadda ake sadar da su. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da:
– sadar da kiɗa daidai da nauyi na muryar makaɗi da kuma raujin da aka zaɓa wa matanin waƙa;
– Dacewar amon kiɗa da gaɓoɓin murya bisa gurabunta na hawa da sauka da kuma faɗuwa;
– Ƙarfafa madirar gaɓoɓi;
– Wani bi a kaurara amon kiɗa;
– Wani bi a sassauta amon kiɗa;
– Wani bi a ja amon kiɗa;
– Wani bi a matse ko a tauye amon kiɗa;
– Wani bi a qwairanta amon kiɗa;
Sannan kuma yanayin kiɗan yana iya zama:
Mai diri
Mai ƙarfi
Mai kauri
Mai zaƙi
Mai kumbura
Mai kaurara
da sauransu
Matakin Rauji
Ƙamus na Hausa a ɓangaren Hausa-English (Awde, 1996: 131) ya bayyana kalmar rauji da clapping wato yin tafi ko ban tafi (Awde, 1996, 131 & 210). A kuma littafin Ƙamus na Keɓaɓɓun kalmomi wato Hausa Metalanguage ya fassara Rauji da Ingilishi da Rhythems wato Kari ko karin murya (Awde, 1996:361).
A fannin ilimin waƙar baka kuwa, rauji wani sauti ko amo ne wanda yake tashi a sama ko ya sauka ko ya faɗi. Rauji yana iya zama murya ta wata halitta mai rai ko sautin wani abu maras rai kamar ƙara ko doka ƙafafu a bisa ƙasa ko wani tsando ko sauti daga kukan tsuntsaye. Har wa yau kuma akwai rauji mai ɗaɗi, mai zaƙi da kuma rauji maras daɗi, mai-ta-da-hankali, kamar kukan kanari (rauji mai zaƙi) da kuma kukan jaki (rauji maras zaƙi, mai ɗaukar hankali).
Wata ma’anar isɗilahi kuma, rauji na iya zama masaukar murya a gaba.
A yayin da aka gwama rauji a waƙar baka ta Hausa ana ɗora shi bisa muryoyi na gaɓoɓi na kalmomi ne waɗanda akan sarƙa su a tayar da saɗara a ɗa na waƙa. Rauji wanda aka zaɓa, aka ɗora wa saɗara ko layi a ɗa na farkon waƙa, shi ne zai dinga daidaita rauji a dukkan layuka da ake ƙullawa a ɗiya na waƙar.
Nauyin rauji a waƙar baka ta Hausa gajere ne, shi ya sa yake tafiya bisa gaɓoɓi na kalma gwargwadon hawansu da saukarsu da faɗuwansu. Matakai waɗanda ake bi a wajen samar da rauji a waƙar baka ta Hausa sun haɗa da:
– Rauji mai dogon zango
– Rauji mai gajeren zango
– Rauji mai matsakaicin zango
Sannan gaɓa ta rauji za ta iya zama mai nauyi wadda za ta ƙunshi [bww] ko [bwb], ko kuma ta zama mai sauƙi wadda za ta iya zama gaɓa mai [bw] kawai.
A wajen furta rauji na waƙar baka ana yi masa waɗannan abubuwa kamar haka:
– Kaurara gaɓa mai nauyi;
– Jan gaɓa mai nauyi ko mai sauƙi;
– Daidaita amsa-amon kari (hawa ko sauka ko faɗuwa) a ƙarshen kowace saɗara ko layi.
Haka kuma ana yin rauji ne na waƙar baka daga karin murya (na hawa da sauka da faɗuwa) da kuma amon kiɗa tun daga tunanin makaɗi a zuciyarsa. Domin haka, ana samar wa waƙoƙin baka rauji ne ta waɗannan hanyoyi:
Karin murya daga makaɗin waƙar;
Amon kiɗa daga kayan kiɗan da makaɗi yake amfani da su, ta la’akari da madiransu na hawa da saukar amo ko kuma faɗuwarsa.
Daga nan sai a fitar mata da raujinta;
Rauji zai samar wa waƙar baka wani amo wanda zai fitar da ita kaɗai daga sauran waƙoƙin baka na makaɗin.
Matakin Kalmomi
Kamar yadda aka nuna a baya, idan makaɗin baka ya tashi aiwatar da wata waƙa ta baka, yakan fara aiwatar da waƙar ne a cikin zuciyarsa da kuma ƙwaƙwalwarsa tun kafin ya furta waƙar a waje. Haka kuma tunanin makaɗi na kalmomi da yadda zai sarrafa su cikin azanci da hikima shi ne wani abu da zai biyo biyo baya a aiwatar da waƙar baka.
Sannan kuma dukkan makaɗi na ƙungiya da kuma makaɗi na ƙire duk suna yin aiwatarwa a wajen daidaita waƙoƙinsu da tsawaita su. Matakin kalmomi yakan bambanta dangane da kalmomi da makaɗi ya yi tunaninsu ko kuma ya zaɓo su wajen tsawaita waƙar da zai yi. Wasu daga cikin kalmomi da ake zaɓa a shirya waƙar baka sun haɗa da:
Kalmomin Shirya Gindin Waƙa
Gindin waƙa furuci ne na wasu kalmomi masu ma’ana masu nauyin saƙo, masu hikima da balaga da azanci waɗanda ake shiryawa don a gabatar da waƙar baka. Ta gindin waƙa ne ake rarrabe ɗa da ɗa a waƙar baka. Waƙoƙin baka sun kasu kashi biyu. Akwai waɗanda ake yi wa Gindin Waƙa kamar waƙoƙin Alhaji Abdu Karen Gusau. Sannan kuma akwai waƙoƙin da ba a yi wa Gindin Waƙa kamar waƙoƙin Alhaji Babangida Kakadawa.
Ga Misali na Gindin Waƙa:
G/Waƙa: A lula ɗan haya,
: Mai gyaran kekuna.
(Abdu Karen Gusau; Waƙar Alhaji Alula Ɗanhayar Kekuna, Fagge, Kano)
Har wa yau kuma, Gindin waƙa yakan bayyana abin da waƙa take nufi tun kafin a shiga cikinta. Gindin waƙa wani ginshiƙi ne ko babban matangali na ginin waƙar baka. Wani kuma harsashe ne ko majingini na farko a waƙar baka, inda duk bai zauna ba, waƙa ba za ta ba da sha’awa ba, balantana har ta yi wani armashi.
Idan makaɗi ya sami zaunuwar Gindin waƙa, to, zai sami haske ya buɗu a gare shi, ya sami walwala ta zaɓo kalmomi waɗanda suka dace ya saka a waƙa waɗanda za su ba shi damar samun sauran ɗiyan waƙar. Makaɗin baka yakan yi tunani a zuciyarsa idan kuma wanda suke a ƙungiya ne sukan haɗa ƙarfi da azama su samo kalmomi zaunannu kuma mafi girkuwa a waƙar da suke shiryawa ta baka su samar da Gindinta.
A wajen shirya Gindin waƙa makaɗa sukan yi amfani da waɗannan matakai:
Yawanci Gindin waƙa bai shige layuka biyu (2) zuwa huɗu (4) ba;
– Yakan ƙunshi kalmomi masu nauyi da ake sarrafa su cikin azanci da hikima;
– Gindin waƙa yakan ƙunshi sunan mai waƙa ko laƙabinsa ko alkunyarsa ko wata ƙarina da ke nuna Mai waƙa;
– Sannan ana wakiltar Gindin waƙa da harafin [X] na ABCD;
– Ana kuma wakiltar adadin saɗaru ko layuka a Gindin waƙa da alkalumma na [1,2,3,4] kamar haka: [X1] ko [X2] ko [X3] ko [X4] da sauransu;
– Ga misalai:
i) Gindin Waƙa; (mai layuka huɗu (4)
X1: Ka bawai maza,
X2: Na Magajin Gari Bubakar,
X3: Kai ad da yanzu,
X4: Allah ya ba ka Sarkin Kabi.
(Mamman Inyaga Argungu; Wakar S/Kabi Muhammadu Mera. Wato kalmomin nuna farin ciki).
ii) Gindin Waƙa; (mai layuka biyu (2)
X1: Tankwafau namijin zaki,
X2: Sa’idu bai taɓa tsoro ba.
(Idi Ɗangiwa Zuru: Waƙar Sarkin Sudan Sa’idu, Kwantagora. Wato kalmomin nuna farin ciki)
– Yawancin kalmomi masu nauyin ma’ana da hikimar zance da makaɗa suke tsarawa a Gindin waƙa sun ƙunshi na nuna farin ciki ko na nuna baƙin ciki. Misalin Gindin waƙa na kalmomin nuna baƙin ciki:
G/Waƙa: X1: Gagarabadon namiji tsayayyen ɗan kasuwa
(Shata: waƙar ‘Gagarabadau, Mp3)
– Kuma wani Gindin waƙar yakan ƙunshi kalmomin yabawa ko na zambo ko na habaici da na zugugutawa da makamantansu. Misali:
G/Waƙa: X1: Ya ci maza ya kwan yana shirye,
X2: Gamda’aren Sarki Tudu Alu.
(Narambaɗa, Waƙar Tudu Alu; Kalmomin zuga da kururantawa da yabawa).
Akwai kuma a wani G/Waƙa:
X1: Madogara na Malam,
X2: Iro Uban Bawa,
X3: Maigida Shinkahi.
(Narambaɗa, Waƙar Magajin Garin Shinkahi, Ibrahim; Kalmomin zuga da yabawa).
– Haka kuma wani Gindin waƙar yakan ɗauki kalmomin faɗakarwa ko gargaɗi ko ilimtarwa ko isharantarwa ko nasihantarwa da sauransu. Misali:
G/Waƙa: X1 “Yan Nijeriya sai Hausa
(Abdu Karen Gusau; waƙar Harshen Hausa-kalmomin kishin Hausa da na gargaɗi da na ilimantarwa. Gusau, 2015: 64-75).
G/Waƙa: X1 Mu kama sana’a ‘yan Nigeriya,
X2 Zaman banza ba namu ne ba.
(Abdu Karen Gusau, Waƙar Gargaɗi kan riƙo da sana’a – kalmomin gargaɗi da na faɗakarwa da na isharantarwa, Gusau, 2015: 75-78).
G/Waƙa: X1 Shegiyar ƙafa ke kika saba da gulando,
X2 Ki tallafe ni, ɗaukar ni ƙafa kar ki gaza ni.
(Abdu Karan Gusau, Waƙar Shegiyar ƙafa – Kalmomin faɗakarwa da na gargaɗi da na isharantyarwa. Gusau, 2015: 96-97).
Layuka ko Saɗaru a Ɗiya
Layuka jam’i ne na layi (tilo). A Ƙamusun Hausa (CNHN, 2016 206-304) an faɗi ma’anarsa kamar haka: (i) Miƙaƙƙen zane (ii) miƙaƙƙiyar hanya ta cikin gari, ko jerin rumfunan kasuwa ko wani abu (iii)majalisar alƙalai ko kotu ko ɗakin shari’a. Amma kuma a ƙamus (Hausa-English) na Awde (1996:106) ya bayyana Layi (p/layuka) da harshen Inglishi da Line. A kuma ɓangaren ƙamus ɗin na English-Hausa, Awde
(1996: 295) ya fassara line da noun=n=: (1) layi (2) Baiti (3) Telephone line wato waya. Ta Fuskar Saxaru (Jam’i); saɗara (tilo) kuwa – Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 381) ya fassara ta da layi cikakke na rubutu.
A cikin layuka ne ko saɗaru waƙar baka take shirya saƙonni tun a ƙwaƙwalwa, sannan ta rera su, ta sadar da su ga al’umma; ta amfani da mataki na kalmomi waɗanda suka haɗa da nau’o’i daban-daban.
Kuma har gami da kalmomi na maganganun habaici da isharantarwa da gargaɗi da ilimantarwa da tunasarwa da faɗakarwa da makamantansu da yawa.
A waƙoƙin baka na Hausa akan shirya layuka ko saɗaru masu sauƙi a ƙagi ɗa na waƙar baka wanda zai ƙunshi saƙo ɗaya kawai. Akwai kuma layuka ko saɗaru da ake shiryawa masu tsauri, waɗanda za su haɗu su tayar da ɗa ɗaya na waƙar baka. Shi ɗa ɗaya mai tsauri yakan ƙunshi saƙonni da yawan gaske kamar guɗa huɗu (4) ko ma fiye da haka waɗanda ake wakiltarsu kamar haka:
Ɗa ɗaya mai tsauri:
A1:
A2:
B1:
B2:
B3:
C1:
C2:
C3:
C4:
Da sauransu. Za a ba da misali na ɗan waƙa mai sauƙi (Mai saƙo guda ɗaya kawai) kamar haka:
A1: Ni kam lafiya nit taho salla,
A2: Lafiya ni ishe Sarki,
X1: Amadun Bubakar gwarzon Yari,
X2: Dodo na Alƙali.
(Narambaɗa, waƙar Sarkin Gobir Ahmadu Bawa (1935-1975).
Shi kuma ɗan waƙa ɗaya mai tsauri (mai Saƙonni da yawa fiye da ɗaya), ga wani misali kamar haka:
A1 Na Magaji mai Martaba ɗan Mu’azu,
A2 Irin assabad Bubakar baba yay yo,
A1.1 Na Magaji mai Martaba ɗan Mu’azu,
A2 Irin assabad Bubakar baba yay yo,
B1 Tsarin gaskiya Bello kai Shehu yac ce,
B2 Bari masu son duk su maishe ka yaro,
B 1.1 Tsarin gaskiya Bello kai Shehu yac ce,
B2 Bari masu son duk su maishe ka yaro,
B3 Da kyauta da ilimi da neman dalili,
B4 Da gode ma Allah da istingfari,
B5 Da su Bello ɗan Shehu yat tsarmo kowa,
B6 Ka kai kamar Bello ka gadi Moyi,
B7 Saura ka kai inda mai Hausa yak kai,
B6.1 Ka kai ka mar Bello ka gadi Moyi,
B7 Saura ka kai inda mai Hausa ya kai,
X1: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,
X2: Sarki Kudu Macciɗo ci maraya.
(Sa’idu Faru, waƙar Muhammadu Macciɗo lokacin yana a matsayin Sarkin Kudun Sakkwato, ya rasu a 1995 yana Sarkin Musulmi).
A layi na ɗan waƙa ana wakiltar sa da alƙalumma na [1-0], da haruffa na ABCD ban da [X] kamar yadda aka gani a misalan da suka gabata. Har wa yau kuma ana iya wakiltar ɗan waƙa ta jan layuka kawai. Misali:
Ɗanwaƙa mai layuka biyu ko uku
Xa: 1 ____________________
2 _______________________
3 _______________________
X1 ______________________
X2 ______________________
Ko ɗa mai layuka biyu
Xa: 1 ____________________
2 _______________________
X1 ______________________
X2 ______________________
Saƙonni a ɗa na waƙa, bisa yawanci ba su shige layuka guda biyar (5). Misali: A1, B1, C1, D1, E1, wato saɗo na ɗaya (1) zuwa na biyar (5).
A layuka ne kuma ko saɗaru ake tunani a zuciya a gina saƙo na farin ciki ko na baƙin ciki ko na faɗakarwa ko na tunasarwa ko na gargaɗi ko na ilimantarwa ko na isharantarwa ko na yabawa ko na zambo ko na habaici ko na wani saƙo da makaɗi yake son ya gaya wa al’ummarsa a harshen waƙar baka.
Alalmisali:
Jarora: Yara farau-farau farar tabarma,
: Farin cikin mai baƙunta,
Y/Amshi: Gagarabadon namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
(Shata, Gagarabadau; Gusau, 2018:20)
Akwai kuma
Jarora: Ga wani ya yi ilimi babu hankali,
: Ga dai ilimi babu nutsuwa,
: An kira shi Dabtan ya amsa,
: Da ganin ƙurji sai ya yaɓa wuƙa,
Y/Amshi: Na gode wa Amadun Gaya.
(Shata, Waƙar Amadun gaya; Gusau, 2018: 23)
A lokacin da makaɗa suke yin tunanin baɗini na wata waƙa da za su shirya sukan bambarta a wajen yin wannan tunani da kuma samo kalmomi na waƙa.
i) Wasu makaɗan sukan zauna a ƙarƙashin wata inuwa kamar ta wata bishiya, su kwanta su lulluɓe kansu, suna tunanin wata waƙa. Alalmisali, Alhaji Ibrahim Narambaɗa, idan yana tunanin waƙa har zana tunanin nasa yake yi a ƙasa, ya dinga shata wani zani ko zane-zane kamar zai zana wani hoto na musamman. Zai dinga zanawa a ƙasa a cikin layuka, ya dinga yin zane-zane, yana tsara saɗaru na waƙa.
ii) Wasu kuma makaɗan sukan dinga jefo wasu kalmomin suna sarƙawa suna kuma zubar da wasu, suna warwarewa, har su haɗa kalmomin da suke buƙata na waƙar. Wasu makaɗan, kamar Salihu Jankiɗi, har tattaka ‘yan amshinsa yake yi, suna zazzaune, idan sun jefo wasu kalmomi da ba su dace ba.
Ta haka dole ɗan amshi ya yi taka-tsantsan da abubuwan da yake ba da tasa gudummawa.
iii) Wasu makaɗan, musamman makaɗan ƙire (kaɗaita) sukan sami saulin yin tunani ne a yayin da ‘yan amshinsa suke maimaita kiɗa, su kuma makaɗan sukan yi shuru, suna numfasawa. A lokacin da kuma sanƙirorinsu suke ba da tasu gudunmawa, su kuwa makaɗan (Jagororin) suna yin shuru, suna saurarensu. Da sauran halayen makaɗan kaɗaita. A duk lokacin da makaɗan suka yi shuru suna tunani ne a kan abubuwan da za su ƙara ƙulla waƙoƙinsu.
Domin karanta cikakken bayani akan Sadarwa a Waƙar Baka danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.
Edita, RMK