Yadda Zaki Kula Da Fatarki

0
41

A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki sukayi yawa a kasuwa,zaɓar abubuwan da zasu taimakawa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan Kika San yanayin fatarki Sai ki zaɓi abubuwan da zakiyi wajen kula da fatarki a kullum.misali:

1.GOGE KWALLIYA KAFIN BACCI

Idan ya kasance an miki kwalliya Mai yawa ta zamani to yana da kyau ki samu abunda Zaki gogeta tas kafin ki kwanta bacci.Koda wacce tayi miki kwalliyar ta ta tayaki gogewa amma Idanuwa  da laɓɓa suna buƙatar kula ta mussamman saboda haka sai ki samu abun goge kwalliya (wiper)jiƙaƙƙe ki sake gogewa a hankali.

Domin karanta Yadda Zaki Inganta Hallayarki Da Ɗabi’u Masu Kyau Danna nan

2.WANKE FUSKA

Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin kiyi kwalliya Sai Kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi bamai zafi ba sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska sannan a sake ɗaurayewa.

3.AMFANI DA TONER

Bayan an wanke fuska anaso a shafa toner a samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan sai ana shafawa a hankali banda gurin ido sannan ba’a wankewa.

Domin karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki danna koren rubutun nan

4.AMFANI DA MOISTURIZER

Bayan toner ta bushe akan fuskarki yana da kyau ayi amfani da moisturizer akan fuska hadda tafin hannu ma idan kinso. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido Sai ki samu wani mai na musamman.

5.YIN MURZA(SCRUBBING)

Ana iyayin murza ta musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati zaki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa sai kina dangwala da hannunki kina murzawa a hankali akan fuskarki.Bayan wasu mintoci sai a wanke da ruwan ɗumi.

6.YIN AMFANI DA (SUNSCREEN)

Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska ko kuma nuna alamun girma.yana da kyau duk lokacin da zaku fita rana ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa akan fatarku.Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

Domin karanta Yadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki Danna nan

labarin da ya wuceYadda Zaki Inganta Hallayarki Da Ɗabi’u Masu Kyau
Labarin na GabaYadda Zaki Nunawa Mijinki Tsantsar Kula
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.