An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Wanda ya zauna a wuri ya yi maganganu da yawa, kafin ya tashi, sai ya ce;
“Subhanakallahumma wa bi hamdika ash hadu an laailaaha illa anta astagfiruka; wa a tubu ilaika”. Za a gafarta masa duk abin da ya aikata a wannan mazauni. (Tirmizi 3433).
Domin karanta cikakken bayani a kan Kasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Tattalin Arziki A Nijeriya danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.