Hadisai da dama sun zo kan bayanin siffofin wutiri kamar haka:
1- Wutri da Raka’a Ɗaya:
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Sallar dare raka’a biyu-biyu ce, idan ɗayanku ya ji tsoron fitowar alfijir, ya sallaci raka’a ɗaya ta zama wutri ga abin da ya sallata”. Kuma ya ce, “Wutiri raka’a ɗaya ne a ƙarshen dare”. (Muslim 752).
2- wutiri da Raka’a Uku: ana yin sa ta hanyoyi biyu:
i. A yi raka’a biyu a yi sallama , sannan a yi wutri a yi sallama. Wannan ya inganta a hadisan Sayyada A’isha da Ibn Abbas da kuma Ubayyu Ibn Ka’ab (R.A) kuma ya inganta cewa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana karanta Suratul A’ala a raka’ar farko, sai Suratul Kafirun a raka’a ta biyu sannan sai Suratul Iklass a raka’ar wutiri.(Bukhari 991, Malik 1/125, ) Tahawi 1/285). Amma karanta Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi, wannan ya zo a Hadisi mai rauni.
ii. A yi raka’a ukun a jere ba tare da an yi zaman tahiya ba, sai a raka’a ta uku. (Bukhari 1147, Muslim 783)
iii. Wutiri da Raka’a Biyar: Ana so ga wanda zai yi wutiri da raka’a biyar ya yi su a jare kada ya yi zaman tahiya sai a raka’a ta biyar. Wannan ya inganta a Hadisin A’isha (R.A) wanda Muslim ya ruwaito.
iv. Wutiri da Raka’a bakwai ko Raka’a tara: Ana so ga wanda zai yi irin wannan wutiri, ya yi su a jere kada ya zauna sai a raka’a ta shida ko ta takwas,sannan ya tashi ya kawo raka’a ta bakwai ko ta tara sannan ya yi sallama. Wannan ya zo a Hadisin. (Muslim 746, Abu Dawud 1328 da Nasa’I 2/199).
Domin karanta cikakken bayani a kan Shin Dole Ne A Yi Shafa’i Kafin Wutiri? danna nan.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.