Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau za mu koyar da yadda ake yin soyayyiyar gyaɗa mai gishiri. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.
Ko kun san soyayyiyar gyaɗa na saurin narkewa a jikin ɗan Adam.
Abubuwan Da Ake Buƙata:
- Gyaɗa rabin mudu (ɓararriyar gyaɗa/mara ɓawo).
- Ƙasa (kamar kofi biyu). Yashi ko toka.
- Gishiri chokali uku
Yadda Ake Haɗawa.
- A tsince gyaɗa mara kyau, ko a bakace gyaɗar, domin fitar da marasa kyau. Sannan a wanke gyaɗar ta fita fes.
- A cikin roba mai zurfi a zuba ruwa, ɗan gishiri da kuma gyaɗar, sai a bar ta kamar na awa 3-4 bayan awannin, sai a tace a busar da shi a inuwa ko rana.
- A zuba ƙasa a cikin tukunya mai zurfi idan ƙasar ta yi zafi sai a zuba gyaɗar cikin ƙasar a yi ta juyawa, har sai gyaɗar ta gasu da kyau.
- Sai a sauke a raba gyaɗar da ƙasa, sannan a bar ta ta sha iska.
Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Taliya danna koren rubutun nan.