Lokuta Da Guraren Da Ake Karɓar Addu’a

0
1268

Yana cikin kamala da girman karamci da rahamar Allah, ya sanya a kowane lokaci, dare da rana, in bawa ya fuskanci Allah ya yi addu’a, to tabbas za a amsa masa.

Tare da akwai wasu lokuta da wurare waɗanda Allah Jalla Wa’alaa ya albarkace su da daraja ta musamman, wanda addu’a a cikin su keda matuƙar tasiri na musamman, ga wasu daga ciki lokutan:

1. Addu’a ranar Arafah.
2. Addu’a a Lailatul Ƙadr.
3. Addu’a a kashi ɗaya cikin ukun ƙarshen dare.
4. Addu’a bayan tahiyar ƙarshe.
5. Addu’a a cikin sujadah.
6. Addu’a tsakanin kiran Sallah da Ikama.
7. Addu’a yayin saukar ruwan sama.
8. Addu’a ranar Juma’a.
9. Addu’a yayin shan ruwan zam–zam.
10. Addu’a yayin da ake kiran sallah
11. Addu’a yayin tashi daga bacci.
12. Addu’a a kwanaki goman farko na Dhul-hijjah.
13 .Addu’a a cikin ka’abah.
14. Addu’a yayin gama karatu ko karantarwa.
15. Addu’a yayin da mayaƙa sukayi sahu.
16. Addu’a a majalissan da ake ambaton Allah.
17. Addu’a yayin da imani ya ƙaru a zuciya.
18 .Addu’a bayan zare ran mamaci.
19. Addu’a yayin jifan Jamraat.
20.Addu’a a kan dutsen Safa.
21. Addu’a a kan dutsen Marwa.
22.Addu’a a Mash’aril Haram.
23. Addu’a yayin ziyarar marar lafiya.
24. Addu’a gabannin sallar azzahar.
25. Addu’a a watan Ramadhan.
26. Addu’a yayin sahur ga mai azumi.
27. Addu’a yayin buɗa-baki ga mai azumi.
28. Addu’a yayin shiga tsanani,matsi da ƙunci.
29. Addu’a da addu’ar zun-nun Alaihis salaam.
30. Addu’a da Istirja’i.
31. Addu’a a multazam.
32. Addu’a a Maƙam Ibrahim.
33. Addu’a yayin karatun suratul Fatiha.
34. Addu’a yayin ƙarfafuwar Mahabbah da Ikhlasi a zuciya.
35. Addu’a yayin carar zakara.
Duba:
1. Du’aa na Dr. Yassir Qadhi
2. ADDU’A WA MANZILATAHU MINAL AQIDATIL ISLAMIYYAH na Dr.JILAN ALARUSIY Wanda rubuntunsa ne na Masters Degree kulliyatud da’awah,Qismul Aqidah a Jami’atul Islamiyyah Madinatul Munawwarah a shekarar 1410A.H
3. Ahmiyyatud Du’a wa Kaifiyyatahu fis Sunnatin Nabawiyyah na Dr.Ibrahim al-Hamd

Domin sannin Alkunyar da ake wa Manzon Allah(S.A.W) danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceYadda Ake Soyayyiyar Taliya
Labarin na GabaYadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri