Yadda ake haɗa Mahshi

0
24

KAYAN HAƊI 

  • Yalon bature (garden egg) 
  • Dankalin Turawa 
  • Albasa 
  • Shinkafa 
  • Niƙaƙƙen nama 
  • gishiri 
  • sinadarin ɗanɗano 
  • Tumatir

Yadda za a haɗ

A sami waɗannan ingredients ɗin na sama(yalon batureda dankali), ki fafe cikinsu duk kansu su yi fale-fale amma ba a yanka su ba, za ki dafa shinkafa ta dahu kaɗan, sai ki kwashe ki saka a cikin kwano. 

Domin karanta yadda ake Fish – Cakes Danna nan 

Idan ta yi sanyi, ki kawo niƙaƙƙen nama ki zuba, naman ya fi shinkafar yawa, sai a zuba shammar da kasbara, ki yayyanka su da garlic da gishiri da maggi ki cakuɗa ya haɗe jikinsa. 

Sai ki wanke kayan da kika fafe, ki tsane ruwansu, ki wanke koren tattasai sai (black pepper) ki zuba a cikin haɗin, ki dinga ɗiban shinkafar da kika haɗa kina zubawa a cikin kayan da kika fafe, ki rinƙa soyawa kaɗan-kaɗan idan kin gama sai ki saka a cikin dagedagen tumatir irin wanda ake ci da kufta.

Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan 
labarin da ya wuceYadda ake haɗa Beef Burgers
Labarin na GabaYadda ake Kabab (V. I P Soup)