Yadda ake haɗa Kufta

0
29

KAYAN HAƊI 

  • Niƙaƙƙen nama 
  • Abin ɗanɗano 
  • Tafarnuwa 
  • Shammar 
  • Masoro 

Yadda za a haɗ

Za a niƙa nama dai-dai yadda ake so, sai a sa masa abin ɗanɗano daidai gwargwado, a sa shammar, tafarnuwa,da masoro, sai a haɗa da mai kaɗan a cakuɗa, ya haɗa jikinsa a shafa a faranti . Sai a riƙa cirar naman ana dundunƙulawa, dogo-dogo sai a soya a ruwan mai me zafi.

Domin karanta yadda ake Fish – Cakes Danna nan 

Miyar da suke ci da Ita. 

Za a iya yi masa miya a ci da ita, a sami markaɗe na tumatur mai yawa, tattasai kaɗan, sai ki zuba a tukunya, ki sa masa ƴar kanwa, ki sa mai, a sa masa tafarnuwa (dakakkiya), a sa abin ɗanɗano, a bar ta ta yi kauri kamar faten doya sai a sa naman a ciki, ya yi minti 1 ko 2 , sai a sauke za a iya ci da dogon biredi.

Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan 
labarin da ya wuceYadda ake haɗa Mulukhayya
Labarin na GabaYadda ake haɗa Gima Macaroni Jallof