KAYAN HAƊI
- Tsakin masara
- Mai
- Zogale
- Sinadarin ɗanɗano
- Albasa
- Attaruhu
- Gyaɗar miya
Yadda za a haɗa
A samu madambaci a zuba ruwa a ƙasan, sai a ɗora ruwan a wuta, sai a wanke tsakin masarar sosai a tsane a mararaki , a sa buhu a saman madambacin, a juye tsakin masara a ciki, a bar shi ya turara kamar awa 1.
A kwashe tsakin a faranti a kawo ruwa a yayyafa masa asa yankakkiyar albasa da attaruhu da sinadarin ɗanɗano da zogale da gyaɗa da mai ɗan daidai misali, a maida shi wuta a dinga yayyafa masa ruwa akai-akai har sai ya turara sosai ya yi laushi sannan a sauke.