Ma`anar Siyasa A Musulunci

0
32
MA’ANAR SIYASA: Siyasa kalma ce ta larabci, watau ‘As-Siyasah”, ma’anarta ita ce tafiyar da shugabancin jama a. Haka nan Larabawa suna amfaní da kalmar a sanda suke nufin shugabanci mai shiryarwa.Watau ba wanda zai kai waɗanda ake shugabantar ga rashin nasara ko halaka ko ɓata ba. 

MA`ANAR SIYASA A MUSULUNCI: 

Ibnu Khaldun ya fassara siyasa a tafarkin Musulunci da cewa, ita ce ɗora kafatanin al’uma a kan mahangar Shari’ar Musulunci, ga abin da yake maslaha ne a gare su (watau abinda zai zama mai amfani a gare su) a lahirarsu; da ma na duniyarsu, wanda amfanin zai koma ga ita lahirar. 

Tunda dai su al’amuran duniya gaba ɗayansu, a wajen Allah, maslahar Su tana komawa ne ga lahira. (lta siyasar Musulunci) a haƙiƙaninta halifanci ce na mai kafa dokoki (watau Allah), game da kare addini da tafiyar da Siyasar duniya da shi. 

Amma malamai sukan ƙara bayani cewa, shugaba zai iya aiwatar da abinda yake maslaha ne, ko da kuwa bai zo ƙuru-ƙuru a cikin Al-Ƙur’ani da Sunna ba. Matuƙar dai bai saɓa wa shi Al-Ƙur’anin ko Sunnar ba. 

Domin karanta Cin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa Danna nan

Abul Wafa’i Ibnu Aƙil ya ce: Siyasa,ita ce aikin da zai sa mutane su fi kusanta abin da yake shi ne daidai, da nisantar ɓarna, koda kuwa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) bai shar’anta shi ba, kuma wahayi bai saukar da shi ba (Ya ce): “Idan faɗinka cewa, babu siyasa sai abin da ya dace da Shari’ ah, kana nufin abin da bai saɓa wa abinda shari’ah ta ce ba, to maganarka ta yi daidai 

Idan har mutum ya fahimci ma’anar siyasa a Musulunci; kamar yadda malamai suka yi bayaninta; zai gane cewa babu bambanci tsakanin addini da siyasa. Siyasa ɓangare ne na addini. Domin shi addini hanyar rayuwa ne gaba ɗaya. Haka kuma mutum zai fahimci cewa siyasa tana da alaƙa da lahira. Ba harka ce ta duniya kaɗai ba.

Domin karanta cikekken littafin  Danna nan 
labarin da ya wuceYadda ake haɗa Dambun Masara
Labarin na GabaAsalin Siyasar Turai Data Musulunci