Asalin Siyasar Turai Data Musulunci

0
29

ASALIN SIYASAR TURAI: 

Game da bayanin asalin siyasar Turai, dole sai an taɓo malamin palsafar nan na Greek, watau Aplaɗun “plato”, wanda ya rubuta littafi mai suna jumhuriya “Republic”, a shekarar 375 BC (watau kafin haihuwar Annabi isa Alaihissalam). Da ɗalibinsa mai suna Arasɗo “Aristotle” wanda ya rubuta littafi mai suna As siyasah “the politics” a tsakanin shekara ta 335 da shekara ta 323 BC, (lokacinsa da ya rubuta mafi yawan Littafansa). 

A cikinsa ne ya yi bincike game da tsarin zamantakewar ɗan ‘adam, tun daga zamantakewar iyali, zuwa zaman gari guda, zuwa na ƙasa da talakawa da dangantakar ita ƙasashen. 

Domin karanta tarihin damokuraɗiyya a Najeriya danna nan

ASALIN SIYASAR MUSULUNCI: 

Ita kuwa siyasar Musulunci ta faro ne tun daga kan Annabi Adamu (Alaihissalam). Shi ne shugaba na farko, wanda ya wakilci Allah a bayan ƙasa4. Sai sauran manzanni, kamar Annabi Nuhu, Annabi Dawud, Annabi lbrahim, Annabi Musa, Annabi Isa da Manzonmu Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) Allah (Subahanahu Wata’ala) yana cewa: 

“Hakika Allah ya zaɓi Annabi Adamu da Annabi Nuhu da iyalin Annabi ibrahim da iyalin Imrana (ya fifita su) a kan sauran halitta( Suratu Ali Imrana, aya ta : 33) 

Domin karanta bayani akan Ma’anar Damokuraɗiyya Danna nan

Abin nufi a nan shi ne, dukkanin manzanni Allah yana aiko su ne domin su tafiyar da tsarin rayuwar al’umominsu kamar yadda Allah yake so. Kowanne annabi za mu ga ba kawai Salla da Zakka da Azumi yake koya wa mutanensa ba. Misali, za mu ga wani yana umarni da cika ma’ auni (kamar annabi Shu’aibu),.Wani yana hana luwaɗi da fashi da makami (kamar annabi Luɗu). Wani yana ƙoƙarin tsamo wani jinsi daga bautarwar wani jinsin (kamar annabi Musa).

Wani ya yi mulkin da babu irinsa (kamar annabi Sulaimanu). Ga kuma annabi Yusufa, wanda ya riƙe wani ɓangare na harkar mulkin ƙasar Masar, da sauransu. Ashe ke nan, asalin siyasar Musulunci gaba yake da na Turai. Ya fi shi daɗewa. Ya fi shi ta wajen kyan asali. Domin shi daga Allah yake.

Domin karanta cikekken littafin  Danna nan 
labarin da ya wuceMa`anar Siyasa A Musulunci
Labarin na GabaShin Damakwaraɗiyya Musulunci Ce?