Yadda Ake Faɗar Ina Ƙaunar ki/Ka A Soyayya.

0
5119

Faɗa wa kogin soyayya abu ne mai sauƙi. Haka ma faɗa wa masoyi ko masoyiya, ina son ka/ki, bai da wahala. Sai dai yakan yi wa masoya wahala idan lokaci yai tsawo.

Musamman a ce kalmar ta dinga tasiri tamkar farkon soyayyarku ne. Kuma lalle akwai buƙatar yawan fadar Ina ƙaunar ki/ka. Sai dai a tabbata da gaske ake. Kuma cikin hanyoyi daban-daban. Niyya da tasirin kalmomin shi ne muhimmi. Shi ke sanya bugawar zuciya. Ya sa shaƙuwa da Bege. Ya haɓaka soyayya ta dinga ƙaruwa.

Muna so a ce dukkan sanda ka fadi “Ina kaunar ki/ka” Ta zama ta sanya farin ciki da harbawa zuciya ga masoyi dake sauraro saboda haka, sai an bi wasu hanyoyi daban-daban. cikin canja salo tare da ‘yan dabaru. Ayyukanka na magana ga masoyiyarka, ba ma tare da furta kalma ba.

Misali:

Wajen kwanaki huɗu (4) kenan, ina cikin ɓacin rai da damuwa. Ni kaina ba zan ce ga asalin matsalata ba. Ina zaune kan tabarma zuciyata cike da jin haushin mai gidana. Na ɗora ruwa zan yi tuwon masara kenan. Sai na ji waya: “kar ki ɗora tuwo yau, ki shirya bayan sallar isha’i za ki raka ni unguwa”. Sai ya kashe wayarsa.
Duk da kasancewar sa talaka, amma yana da ƙoƙari akan gidansa. Sai dai kuma ba ya birge ni.

Tunani na fada: unguwa kuma? To ina za mu? Wani abu ne ya faru a gidansu Goggo? Nan da nan na canja kaya. Ina idar da sallar isha’i kuwa ,sai ga shi. Yai mana shatar a-daidaita ( Opay ). Bayan mun zauna na ce lafiya kuwa ? Ya ce, “ƙalau”. Sai ya kamo hannuna ya ɗora a kan cinyarsa. Kawai sai na ji wani sanyi a raina. Yana riƙe da hannuna har muka isa Yahuza Suya. Ya biya a-daidaita ta cikin waya. Muka sauka ya ce zo mana.

Ya nuna min kujerun waje na daidai shuke-shuke. Shi kuma ya wuce wajen siyayya. Sai ga shi da kaza da lemo ( ice cream ). Ya buɗe muna ci. Sai ya sa hannu a aljihunsa. Ya ce miƙo hannunki. Sai ga shi ya ɗora min wata guntuwar takarda .

Cikinta ya rubuta da kansa : “INA KAUNARKI SOSAI, A MATA BABU IRINKI” Habawa sai na jawo hannunsa na dinga sumbata ba adadi! Na Ƙara ƙura wa takardar nan ido, ina riƙe da hannunsa gam. Har sai da na ji hawaye sun fara gangarowa a kumatuna. Kawai na miƙe na faɗa jikinsa. Sai ya ce ke: “Mutane na kallon mu”. Ni kuwa nai kamar ban ji ba. Bayan na gama juye-juyena a jikinsa. Na ɗago na ce: “Wallahi na ji daɗi sosai. Sai na ji nan da nan zuciyata ta cika makil da soyayyarka. Na gode ƙwarai. Muna gamawa kuwa, ya zaro waya ya ƙara mana shatar a-daidaita. Muna shiga na kwanta jikinsa, ya riƙo ni, har muka isa gida. Sai na killace takardata da kyau. A koda yaushe ganinta na tuno min da fitarmu. Kuma inji wani sabon farin ciki. Gaskiya da na ɗauka ma, mijina bai iya soyayya ba. Shi ya sa sam ba ya birge ni a can baya.To kun ga akwai ayyuka da dama da su ka wakilci “INA ƘAUNARKI SOSAI” A wannan labari. Wato yin furuci Aiki. Soyayya Ingantacciyya.

HANYOYIN FADAR INA KAUNAR KI/KA:

LOKUTA : Masoya su dinga fadar ina kaunarki a lokuta daban-daban.
1 -Da safe za a rabu ( zai je aiki).
2 – Lokacin haɗuwa ( yana shigowa gida).
3- Lokacin da za a yi barci.

YARE : Amfani da yare kala-kala wajen faɗar Ina sonki. Larabci , da fulatanci , da Barbanci , da Yarbanci , da dai sauransu.

Larabci : Uhibbuki
Fulatanci : Mi yidi ma
Barbanci : Nya Raina
Yarbanci : mo nife re
Inyamuranci : a hurum gi n’anya .
Turanci : I love you

WURARE : Canja wurare daban-daban koyaushe, Ka fada a ɗaki, anjima ka same ta a madafa ( kitchen) . In za ka fita a bakin ƙofa. In ka ajiye ta a unguwa.

RUBUTU : Rubuta kalmar ina kaunar ki/ka.
1 – A rubuta da rubutun ka/ki a takarda ko wani kwali ( cardboard paper) a ba wa Masoyi ya/yi.
2 – Tura ma masoya ta waya. A sakon kar-ta-kwana (text message) .
3 – Katin soyayya ku siya ku ba wa Masoyanku.

HOTUNA : Tura hoton filawa , zuciya , tsuntsaye mai jan hankali. Da mai haɗe da kalmomin soyayya. Ta cikin Hanyoyin yanar gizo ( email , Whatsapp, …).

KYAUTA : Kyauta babbar alama ce ta soyayya. Ana son ba da kyauta daga lokaci zuwa lokaci. Misali : Turare , sutura, zobe , agogo , da dai sauransu.

A ƙarshe dai dukkanin waɗannan da ma sauran irin su. Ayyuka ne dake fassara cewa :” Ina KAUNARKI / KA”. Kun ga ɗaukar su da muhimmanci. Da sabawa da yin su a cikin rayuwarmu zai dinga haɓaka soyayyarmu.

Litattafai da aka duba:
1 – Islamic Education.
By Iqraa charitable society. Jeddah, Saudi Arabia.

2 – 101 Amazing ways to say “I love you ! “.
By Cucan Pemo.

labarin da ya wuceKhuɗubar Annabi (SAW) Ta Ban-Kwana
Labarin na GabaHausawa Da Al’adunsu
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.