Khuɗubar Annabi (SAW) Ta Ban-Kwana

0
1737

Manzon Allah(SAW) ya fita daga Madina tare da Sahabbai dubu 14 a ranar Asabar 26 ga watan Zulqidah a shekara ta goma bayan Hijirah da nufi yin aikin Hajji.

Annabi (SAW) ya fita Zuwa Mina ranar 8 ga watan Zul-Hijjah na wannan shekara ta 10, inda ya isa filin Arfa ranar 9 ga wata.

A wannan rana ma’aikin Allah (SAW) ya yi khuɗuba mai girgiza zukata, kuma mai sanya idaniya ta kwaranyar da hawaye daga cikin abin da yake cewa shi ne:-

“Ya ku mutane, mai yiwuwa ne ba za mu sake haɗuwa da ku a nan ba daga yau. Ya ku mutane kada ku koma(kamar) kafirai a bayana sashinku yana saran wuyan sashinku

……” Ya mutane! Yau wace rana ce? Sai sahabbai duka suka ce “Yau rana ce mai alfarma(daraja) sai Manzon Allah ya sake cewa “Wannan kuma wane gari? Sai suka ce garin (Makka)ne mai alfarma. Sai Annabi ya sake tambayarsu cewa “Shin wane wata ne wannan? sai suka ce wata ne mai alfarma. Sai Annabi(SAW)ya ce, “Ku sani cewa dukiyoyinku da jinananku da mutuncinku haramun(alfarmar daraja) ne a tsakaninku kamar haramcin wannan rana taku, a wannan wata naku a cikin wannan gari naku.
“Ya ku mutane ina yi muku umarni da kyautatawa matanku da abin da hannayenku suka mallaka (na bayi). “Ya ku mutane ban ji tsoron za ku koma kafirci a bayana amma ina jin tsoron a shimfiɗa muku duniya ku zo kuna yin rigima a kanta kamar yadda waɗanda suka zo gabanin ku(Yahudu da Nasara) suka dinga rigima a kanta a tsakaninsu. Sai ya yi ta maimaitawa, har daga ƙarshe ya ce da su “Shin na idda saƙo? Suka ce na’am. Shin na idda saƙo? suka ce na’am. sai ya ɗaga hannayensa masu albarka sama ya ce, “Ya Allah ka shaida.*Ya Allah ka shaida

Daga nan ne Annabi (SAW) ya koma Madina bayan kammala aikin hajjinsa na ban-kwana.

Za mu ci gaba insha Allahu. Allah ya sa mu dace

labarin da ya wuceYadda Za Ki Ratsa Yatsunki Cikin Na Mai Gidanki
Labarin na GabaYadda Ake Faɗar Ina Ƙaunar ki/Ka A Soyayya.