Dukkan godiya da ɗaukaka Ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata a kan Manzonmu Annabi Muhammad SAW, tare da Alayensa da sahabbansa masu girma.
Haƙiƙa ‘yan Uwa Musulmai; babu wani abu da zamu yi wa Ubangiji sai dai godiya bisa ni’imominsa da ya yi mana masu yawa, daga ciki sun haɗa da wannan wata mai Albarka wanda ake aiwatar da wasu muhimmun ibadu kamar Haka:
i. Akwai kwanaki goma na farkon wata wanda Allah SWT ya yi rantsuwa da su domin girmansu inda yake cewa:
“Na rantse da Alfijir, Da kuma kwanaki goma (na farkon watan Dhul-Hajj.)”
Sannan ya tabbata daga Ibn Abbas (R.A) yace “Babu wasu kwanaki da ake aikin alheri a cikinsu (Aikin lada) wanda ya fi soyuwa a gurin Allah SWT fiye da waɗannan kwanaki goma na Farkon Wannan wata (Dhul-HaJJ) Sai sahabbai suka ce: Har yaƙi don ɗaukaka kalmar Allah? Sai yace: Har yaƙi don ɗaukaka Addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyar sa, sannan bai dawo da ɗaya daga cikinsu ba (Dukiya ta ƙare; shi kuma ya yi shahada). Bukhari.
ii. Daga cikin falalan wannan watan babbar Sallan (Dhul-Hajj) akwai Ranar Arfa wanda ya zo a hadisin Manzon Allah SAW yace: “Duk wanda ya yi Azumin ranar Arfa; Allah zai gafarta masa zunubansa na shekara biyu (shekarar da yake ciki da kuma shekara mai zuwa). Bukhari
iii. Yawaita ‘yanta bayi daga wuta zuwa aljanna. An karbo daga Nana Aisha (R.A) tace: Manzon Allah SAW yace: ‘Babu wata rana da Ubangiji SWT ya fi ‘yanta bayi daga cikin wuta kamar ranar Arfa” Muslim.
YANKAN LAYYA
Manzon Allah SAW yace: Dabbar da ɗaya daga cikinku zai yanka saboda layya yana da Hasana ga kowanne gashi. Saboda haka ‘yan uwa musulmai mu yawaita aiki na ƙwarai a cikin waɗannan kwanaki Musamman ranar Arfa, sannan mu yawaita Addu’a da neman gafara da shiriya da neman arzikin duniya da Lahira. Sannan mu roƙawa ƙasarmu zaman Lafiya da kuma shugabanni na kwarai.
KWAƊAITARWA A KAN LAYYA
Layya sunna ce mai ƙarfi, sannan ta samo asali ne tun daga zamanin Annabi Ibrahim, inda Allah ya yi masa Umurni (a cikin Mafarki) ya yanka dansa (Annabi Isma’il) wanda ya daɗe yana neman Haihuwa Allah bai ba shi ba, sai daga baya ya samu wannan ɗan (Annabi Isma’il). Ku duba irin soyayyar da ke tsakanin ɗa da uba, amma don cika umurnin Allah, sai ya faɗawa ɗan; sai ɗan yace: Ya baba ka cika Umurnin da Allah Yayi maka. Annabi Ibrahim ya kama ɗansa (Annabi Isma’il) ya kwantar da shi, ya sa wuƙa zai yanka shi. Sai Allah ya canza mashi da Rago.
Danna nan don karanta Gudumawar Iyaye Wajen Gina Al’umma
Edita@rumasau-kallamu