Yadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread)

0
895

Barkanmu da sake kasancewa acikin shirinmu na Girke-Girken WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tareda bayani akan lafiyarsu cikin harshen hausa a saukake tare dani Hafsat Shettimah.

A yau zamu koyar da yadda ake yin Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread); ku biyoni a sannu domin mu koya tare……

Ko kun san Gyada na ɗauke da sinadarin protein wanda ke taimako wurin gina jikin mu.

Abubuwan Da Ake Buƙata

  1. Fulawa kofi 3
  2. Bota ¼ kofi
  3. Fulawar gyaɗa (Groundnut flour) kofi ɗaya
  4. Yis (Yeast) ƙaramin cokali 1
  5. Bakin hoda I (Baking powder)1 rabin ƙaramin cokali
  6. Ƙwai guda 1
  7. ½ rabin kofin siga
  8. ½ rabin ƙaramin cokali na gishiri

Yadda Ake Haɗawa

  1. A zuba ruwa a kofi, sai a zuba yeast da sugar a juya abarshi kamar minti 3-4.
  2. A haɗa sauran kayan haɗi (flour, butter, ƙwai, fulawar gyaɗa, gishiri). Kar a manta a chakuɗa sosai.
  3. A zuba ruwan yis sai a ɗan ƙara ruwan ɗumi a cakuɗa har sai ya haɗe jikinshi. Note:- ya ɗan fi kwaɓin cincin amma karya kai na fanke tsaka-tsaki.
  4. A sami film ko tsumma mai kyau a rufe a kai shi rana ya tashi sai ayi punching tsakiyar iska ya fita sai abarshi ya ƙara tashina minti uku zuwa huɗu.
  5. A yayyanka a sakashi a cikin gwangwanin gashi da aka shafa bota da flour. A ƙara barin shi ya tashi.

A saka biredin cikin abun gashi sai yayi golden colour. Temperature 1800c.

Domin sanin yadda ake kek ɗin gyada danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Kek Ɗin Gyada (Groundnut Cake)
Labarin na GabaYadda Ake Donut
BHM Ninja
Sunana Buhari Ibrahim Aliyu [Googler] dalibin computer, digital marketer, technical crew a wikihausa dalibi mai kokarin yada ilimi na na'aura mai kwakwalwa tare da tabbatar cigaban kasuwancin zamani.