A yau za mu koyi yadda ake coconut jollof rice.
Abubuwan da ake buƙata:
- Garin kwakwa ko markaɗaɗɗiyar kwakwa
- Shinkafa
- Karas
- Koren tattasai
- Koren wake ƙanana (Peas)
Yadda ake haɗawa
- A dora ruwa a wuta. Idan ya tafasa, sai a zuba shinkafa har sai shinkafar ta tafasa na tsawon minti 15 sannan sai a wanke da ruwa a sa a matsami a ajiye.
- A kankare karas, sannan a wanke kafin a yayyanka shi ƙanana. A wanke tattasai da koren wake da koren kanana (Peas) sai a yayyanka su, amma ban da (Peas) din.
- Bayan an kankare bayan kwakwar an markada farin, sai a zuba ruwa sosai. Da ruwan kwakwar za ayi sanwar dahuwar.
- A zuba ruwan kwakwar a tukunya bayan ya tafasa sannan a zuba wannan ajiyayyen shinkafar idan ta kusa dahuwa, sai a zuba yankakken koren tattasai da karas da koren wake, da kuma koren wake ƙanana (Peas) a rufe da murfi a rage wutar girkin.
- Bayan mintuna biyar, sai a gauraya wannan shinkafar a sauke. Shi kenan an kammala.
- Ko da maigida ba mai son cin shinkafa ba ne, za ki ga ya fara sha’awar cin irin wannan girkin. Za a iya haɗa wannan girkin da miyar kaza ko miyar kifi.