Malam Mubammad Sani Ɗan Tudu (1882-1979)
An haifi Malam Muhammad a shekara ta 1882 a Dabai. Mahafinsa Andi shi ne Sarki Zuru na Biyar. Asalin Musuluntarsa shi ne, tun yana yaro ƙarami an taɓa sace shi, wata tsohuwa ta saye shi ta sa masa suna Muhammad. Mahaifinsa ya yi ta nemansa har ya fidda rai.
Malam Muhammad ya yi makarantar Alƙur’ani a garin Kermi da Gwandu da Jega da Kambaza.
Cikin shekaru biyu ya kammala karatun AIƙur’ani. Malam Muhammad ya dawo gida ya gaji sarautar Sarkin ƙasa har tsawon shekaru huɗu a shekara ta 1960. Ya canja sunan sarautar izuwa Marafan Dabai domin Ubangiji Maɗaukaki Shi kaɗai ne Sarkin ƙasa.
Malam Muhammad ya yaɗa koyar da Alƙur’ani a Dabai a shekara ta 1923 a inda ake koyawa manya da yara Alƙur’ani. Wannan ya taimaka gaya wajen shigowar ‘yan ƙabilar Dakkarawa Musulunci. A shekara ta 1946 aka naɗa Alaramma Malam Muhammad Sani Sarkin Zuru a lokacin yana hakimin lardin Dabai.
Irin himmarsa wajen yaɗa Musulunci ta hanyar buɗe makarantun Alƙur’ani ya kawowa makarantun boko da na mishan (missionaries) tasgaro wanda ya kai ga rushewarsu. Misali, makarantar mishan ta Mahuta an rufe ta a shekara ta 1963 bayan ta shekara bakwai babu wata nasara.
Malam Sani ya mulki Zuru daga shekara ta 1946 har zuwa shekara ta 1960 lokacin da aka tuɓe shi a bisa wasu dalilai na siyasa. Bayan ya yi murabus ya koma Mina ya shekara goma sha bakwai. Daga baya ya dawo Dabai a shekara ta 1977. Malam Sani ya rasu a shekarar 1979. Cikin ‘ya’yansa akwai mashurin malamin nan Alhaji Bello Dabai.
Malam Aliyu Maiwa (1868-1974)
An haifi Malam Aliyu a Unguwur Rimi (Deng-re) da ke Zuru a shekarar 1868. Ya karɓi Musulunci a shekarar 1894. Ya fara koyon hukunce-hukuncen ibada da Alƙur’ani a wurin malaminsa Malam Umar a shekarar 1920. Daga nan sha’awar neman sani ta motsa shihar ya yi tafiya izuwa Kwantagora. Daga nan kuma ya dangana da Zungeru wurin Malam Garba Langa-langa da Limamin Zungeru Aliyu.
Koda Liman Aliyu ya ga irin kwazon Malam Maiwa da kaifin basirarsa, sai ya tafi aikin Hajji da shi a shekara ta 1926 An ce kafin dawowarsa daga Makka, tuni ya kammala haddace Alƙur’ani, domin kuwa ya tsaya a Barno ya duƙufa wajen tilawa da ƙwami.
Saboda baiwar rubutunsa kuwa, hukumar lardin Zuru ta sayi kwafen Alƙur’anin da ya rubuta da hannunsa aka buga don amfani da su a ɗakunan Sharia’a a Zuru A matsayinsa na ɗan ƙabilar Dakkarawa wanda ya Musulunta kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa Addinin Musulunci a yankin.
Domin karanta cikakken bayani akan Birane Garuruwan Da Suka Shahara Da Tara Makaranta Da Tsangayu A Arewacin Niajerijya danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan DUNIYA MAKARANTA! danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.