Tatsuniyar Sarkin Maƙera Da Dodo

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku. A wani ɗan ƙauye, an yi wata mata mai ’ya’ya biyu, mace da namiji. Sunan namijin Fugo shi ne wa; ita kuma macen sunanta Awa, ita ce ƙanwa. Shi Fugo maƙeri ne. Ana nan, sai wata rana wani mutum daga wani gari mai nisa ya zo ya ce yana son ya auri Awa, sai aka yarda, aka ba shi ita.

Bayan an gama biki, sai ya ɗauki matarsa suka tafi garinsu, wanda ba a bin hanyar zuwansa da rani saboda akwai wani dodo da kan tsare hanyar, ya cinye matafiya duk lokacin rani. Amma kuma da damina ba ya taɓa kowa. Ana nan, ana nan sai a wata damina Fugo ya je garin mijin ƙanwarsa Awa don ya gaishe su.

Bayan ya dawo da rani sai mahaifiyarsu ta rasu, kuma ana so a aikawa Awa garin da take aure, to amma ba hali saboda a cikin rani ne; kowa yana tsoro kada ya bi hanyar dodon nan ya cinye shi. Ana cikin neman mai zuwa, sai kurciya ta ce za ta je ta gaya wa Awa saƙon. Sai ko aka ba ta saƙo, ta tashi sama, ba ta sauka ba sai a kan ɗakin Awa.

Awa na kwance a ɗaki, sai ta ji kurciya tana waƙa, tana cewa:

“Awa, Awa kina barci,

Ga uwarki can,

Tana barci tun shekaran jiya,

Tun shekaran jiya ba ta tashi ba,

Ki shirya, za ki dakan gero.”

Sai ta fito ta saurara da kyau, ta fahimci lafazin waƙar kurciya, sai ta fashe da kuka, har da kururuwa. Da mijinta ya ji, sai ya shigo ya tambaye ta abin da ya faru. Sai tace an aiko mata da rasuwar uwarta ne. Da ya ji haka sai yace: “To, ga shi hanya ba za ta biyu ba. Yanzu yaya za a yi?”

Duk da cewa Awa ta san dodo yana hanya kuma tabbas idan ta bi hanyar zai cinye ta, sai ta ce ita kam lallai sai ta je ta gano kushewar mahaifiyarta tun ba ta daɗe da rasuwa ba. Da mijin Awa ya lura lallai ta tsaya kai da fata sai taje, sai ya ce: “To, shi ke nan, sai mu yi wata dabara, mu yanka miki shanu, mu raba su gida bakwai, idan dodo ya taso zai
cinye ki, sai ki jefa masa kashi ɗaya.

Da haka har ya ƙoshi, ke kuma ki isa gida.” Sai Awa ta ce: “To na gode, mai gida.” Aka kama shanu, ya yanka, ya sa aka kasa nama gida bakwai, aka zuba wa Awa a cikin masaki. Da ranar da aka sa ta zo, sai ta kama hanya, ɗauke da masakin nama. Tana cikin tafiya a daji, sai dodon nan kwatsam ya ɓullo, yana tafiya yana waƙa, yana cewa:

“Maraba, lale, lale,

Wannan mata, lale,

Ina za ki je?

Gaya mini, ina za ki je?”

Dodon nan baƙi ne ƙirin, ga gashi duguzunzun; abin gwanin ban tsoro. Idan ya buɗe baki sai turiri ke fita. Amma Awa ba ta tsorata ba, sai kawai ma ta mayar masa da waƙa:

“Ni Awa, ni Awa,

Zan je makokin mutuwa,

Mutuwar uwata,

Zan je kai kayan mutuwa,

Mutuwar uwata,

Zan kai kayan miya,

Kayan miyar mutuwar uwata.”

Sai dodo ya matso kusa da ita ya ce: “Buɗe in gani; menene a ciki?” Da ta buɗe masaki ya ga naman sa ne, sai ya ce: “Ko dai ki ba ni ko in haɗiye ki.” Sai ta ce: “Idan ka haɗiye ni zan yi maka kuka.” Sai dodon ya ce: “Yi kukan mu ji.” Sai ta ce:

“Wai, wai, wai, Gari ya yi zafi,

Uwata ba ta nan,

Uwata ta tafi lahira.”

Tana gama waƙar, sai ta ɗauki yankan nama ɗaya ta jefa masa. Da ya tsaya yana ci, sai ta kama hanya tana sauri. Kafin ya cinye ta yi nisa. Da ya cinye, sai ya sake bin ta, ya sha gabanta ya kama waƙa, ita kuma sai ta mayar masa. Duk sanda ta jefa masa naman, sai ta fara gudu, shi kuma ya ɗauki naman ya tsaya ya cinye.

Da ya cinye sai ya sake bin ta. Haka suka rinƙa yi, har naman ya ƙare. Ba ta yi
nisa ba sai ta yar da masakin, ta kama gudu. Shi kuma da ya cinye nama, sai ya bi ta. Da ta ga dai ya kusa kamo ta, sai ta hau bishiya, shi kuma ba zai iya hawa ba; sai ya tsaya a gindin bishiyar.

Can sai ya ɗaga kai ya ce da Awa: “Ki sauko in cinye ki”. Ita kuma ta rasa yadda za ta yi, sai kwatsam ga kurciya ta sauka a kan bishiyar. Sai Awa tace da ita: “Idan na aike ki wurin yayana me za ki ce da shi?” Sai kurciya ta ce: “Zan ce da shi Fugo kana maƙera kana ƙira, amma ƙanwarka tana can a kan bishiya dodo zai cinye ta a dokar daji.”

Sai Awa ta ce da kurciya: “Yawwa, haka za ki je ki faɗa masa.” Nan take kurciya ta tashi sama, ba ta tsaya a ko’ina ba sai kan bishiyar da ke kusa da maƙerar Fugo. Da saukarta ta fara waƙa tana maimaita saƙon da aka aiko ta sanar wa Fugo. Da ya ji waƙa, sai ya ɗaga kansa sama, ya ga kurciya, ya kuma fahimci abin da ta faɗa.

Sai ya shiga shiri, domin bai ga ta zama ba, saboda dodo zai kashe masa ƙanwa. Ya ɗebi makamai irin waɗanda yake ƙerawa, kamar masu da kwari da baka da takubba da sauransu, ya kwance karnukan farautarsa guda goma, sai ya ce da kurciya ta tashi sama, zai bi inuwarta har gindin bishiyar da dodo ya tsare masa ƙanwa.

Haka Fugo ya kama hanya, kurciya na yi masa jagora. Idan ya saki hanya, sai ta yi waƙa, shi kuma ya bi inda ya ji muryarta, har dai suka isa. Suna zuwa, sai suka tarar da dodon a inuwar bishiyar yana barci. Ba tare da jinkiri ba, sai Fugo ya zaro kibiya ya ɗirka wa dodon nan. Kafin ya farka, sai da Fugo ya yi masa ruwan kibau kamar ashirin.

Da ya farka, kafin ya wartsake Fugo ya jefa masa masu kamar guda tara. Amma duk da haka da ya wartsake sai aka ji yana cewa: “Kai wane cinnaka ne yake damuna?” Shi kuma Fugo sai ya zaro wasu kibau masu dafi, ya dinga ɗana su yana sakar wa dodo ɗaya bayan ɗaya a idonsa na dama, nan take idonsa ya tsiyaye.

Kafin ya san abinda ake ciki, Fugo ya sake auna ɗaya idon, kuma ba kuskure ya same shi. Shi ma nan take ya tsiyaye, dodo ya zama ba ya iya gani. Tuni dafin kibiyar ya bi jikin dodo, har ya zamanto ba zai iya tashi ba. Sai Fugo ya ce da Awa ta sauko. Sai dodo ya ce: “Ki sauko in cinye ki.” Da Fugo ya ji haka, sai ya zare takobi ya sassare dodo, ya yi masa gunduwa-gunduwa.

Awa tana gani, amma da ta yunkura za ta sauko, sai guntayen naman dodo suka ce, idan ta sauko za su cinye ta. Da Fugo ya ga haka sai yasa karnukansa suka cinye naman dodon gaba ɗaya, sannan ya ce ƙanwarsa ta sauko. Da ta miƙo ƙafarta za ta sauko, sai ƙasusuwan suka ce, idan ta sauko za su cinye ta. Sai ya sake sa karnukansa suka cinye ƙasusuwan.

Daga nan kuma ta sake miƙo ƙafarta za ta sauko, sai busasshen jinin dodon da ke ƙasa ya ce, ta sauko ya cinye ta. Daga nan dai sai Fugo ya sa karnukansa suka gwaguye jinin da ya yi kasko a ƙasa, har dai suka tabbatar babu kome a wurin, sai ya ce to ta sauko. A nan ne fa ta sauko lafiya, yasa ta a gaba, suka kama hanyar gida.

Nan da nan labari ya bazu cewa Fugo Sarkin Maƙera ya kashe dodo, kuma hanya ta yi lafiya, rani da damina, babu sauran fargaba. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Haƙuri da juriya da nuna jarumta sukan sa a shawo kan matsala komai tsaurinta.
  • Farar aniya laya.
  • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha-maza-ha-mata sai ya gani.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Umbagila Da Dodo

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Umbagila Da Dodo
Labarin na GabaTatsuniyar Sandar Arziƙi
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.