Tag: ilimi

  • Addu’ar Tashi Daga Majalisi

    Addu’ar Tashi Daga Majalisi

    Addu’ar Tashi Daga Majalisi (Domin Neman Yafewa Ga Abin Da Ya Gudana A Cikin Majalisin).

    A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam), bai taɓa zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alƙur’ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da waɗannan kalmomi:

    “Subhaanakal laahumma wa bi hamdika ashhadu an laa ilaaha illaa anta astagfiruka wa atuubu ilaika”.

    {Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah, da yabo gare ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai; ina neman gafararka, kuma ina tuba zuwa gare ka}.

    Sai A’isha ta ce:- “Ya Manzon Allah! Na lura cewa ba ka taɓa zama a wani majalisi ba, ka yi karatun Alƙur’ani, ko ka yi sallah face ka faɗi waɗannan kalmomi. Sai ya ce: “Ƙwarai. Duk wanda ya faɗi wani alheri sai waɗannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya faɗi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi”.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’a A Lokacin Da Mutum Zai Haw Abin Hawa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Edita; RMK

  • Addu’ar Komowa Daga Tafiya

    Addu’ar Komowa Daga Tafiya

    Abdullahi ibn Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga tafiya wani yaƙi; ko aikin hajji ko umara, idan ya hau tudu sai ya yi kabbara sau uku; sannan ya ce:

    “Laa ilaaha illallaahu wahdahu laa shariika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun, aayibuuna taa’ibbuna, aabiduuna li rabbinaa haamiduuna, sadaƙal laahu wa’adahu, wa nasara abdahu wa hazamal ahzaaba wahdahu”.

    {Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai; babu abokin tarayya a gare shi. Mulki nasa ne (shi kaɗai); kuma shi mai iko ne a kan komai. Mu masu komawa ne, masu tuba, kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu. Allah Ya gaskata alƙawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai shi kaɗai}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Tafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Edita; RMK

  • Addu’ar Mazaunin Gida Ga Matafiyi

    Addu’ar Mazaunin Gida Ga Matafiyi

    “Astaudi’ul laaha diinaka wa amaanataka, wa khawaatima amalika”. {Ina ba wa Allah ajiyar addininka, da amanarka, da ayyukan da ka ke cikawa a kan su}.

    “Zawwadakal laahut taƙ’waa, wa gafara zanbaka wa yassara lakal khaira haisu kunta”.

    {Allah ya yi maka guzurin taƙawa, ya gafarta maka zunubanka, ya sauƙaƙe alheri gare ka a duk inda kake}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Tafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Yin Salatut Tasbihi danna nan.

  • Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare

    Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare

    Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; ‘Idan kuka ji haushin karnuka, da kukan jaki da daddare, to ku nemi tsarin Allah daga gare su; don kuwa su suna ganin abin da ba kwa gani’.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Yaɗa Sallama A Cikin Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Munafuntar Al’umma Da Rashin Fayyace Alƙibla danna nan.

    Don karanta Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan

  • Waƙar Ilimi

    Waƙar Ilimi

    Waƙar ilimin zamani ta Mu’azu Haɗeja

    1. Gishiri in ba kai ba miya,
    Ilimi mai gyaran zamani.

    2. Jama’armu ku jawo hankulanku,
    Mu lura da halin zamani.

    3. Iko, mulki, ƙarfi, duka,
    Na ga wanda ya ƙaddari zamani.

    4. Ilimi shi ke gyaran ƙasa,
    Har a santa a wannan zamani.

    5. Babu jin kunya gun mai limi,
    Jahili shi ke ta wuni-wuni.

    6. Yanda kaska ke tsotsar jini,
    Haka jahilci gun zamani.

    7. Da tsiya da talauci duk suna,
    Gun da jahilci ya yi sansani.

    8.Wa’azinmu ga mai karɓa duka,
    Masu murnar gyaran zamani.

    9. Masu son lardinmu ya ɗaukaka,
    Bisa kan juyawar zamani.

    10. Kar su fara faɗar da-na-sani,
    Da mun yi karatun zamani.

    Allah ya gafartawa Malam Mu’azu Haɗeja da sauran magabata.

    Danna nan don karanta saƙo cikin waƙa

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Yadda Za Ki Inganta Halayyarki Da Ɗabi’u Masu Kyau

    Yadda Za Ki Inganta Halayyarki Da Ɗabi’u Masu Kyau

    A matsayinki na mace kuma uwar gida (mai zaman aure); Ya kamata ki san irin halayya da ɗabi’u masu kyau da za saba da su.

    1. Ƙwarin Gwuiwa

    Zaman Aure -Idan ya kasance ba ki da ƙarfin gwuiwa akan kanki ƙarfin zuciya hakan zai sa ki zama ba kya birge mijinki. Kuma zai hana ki samun jituwa da kyautata mu’amala, ki dinga faɗawa kanki cewa ke kyakkyawa ce, kina da kyakkyawan ɗabi’u. Kuma mijinki na sonki ne saboda halayyarki masu kyau.

    2. Kula Da Kanki

    Kulawa ba wai ta wanka da kwalliya ba a a ki ɗauki al’amuran da ya shafi yadda kike ji a zuciyarki da muhimmanci, farin ciki ko baƙin ciki saboda a duk lokacin da mijinki ya ɓata miki ba zai sa alaƙarku ta lalace ba. Kuma yana da kyau ki rage ɗaurawa kanki laifi akan komai. Hakan na da wahala amma idan kina samun lokaci da ‘yan uwanki ko kawayenki ko kuma kina iya koyon wasu abubuwan sababbi, da kuma wasu abubuwan da kike son yi kamar zane, rubutu ko karance-karance.

    3. Tarayya

    Kar ki ɗau mijinki ba a bakin komai ba, ki nuna masa muhimmanci da girmansa a rayuwarki. Ki samar masa da lokaci a cikin ranakun aiki da za ki dinga tattauna abubuwan da suke faruwa da ku. Ko ki dinga tura masa saƙo ko kiran waya sau ɗaya ko sau biyu wanda zai nuna masa cewa kina tare da shi kuma kina tunaninsa a ranki.

    4. Neman Taimako

    A kan aikin gida yana da matuƙar wahala kula da miji da kuma larurar gida musamman idan kina da yara. Hakan zai sa ki gaji kuma ki kasa samun lokacin kanki. Za ki iya samun sauƙin abubuwan ta hanyoyi kamar haka: Nuna masa yadda ake aikace-aikacen gida da kula da yara, samun mai kula da yara ko kuma mai gyaran gida.

     

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Zaku Gyara Zamantakewarku Ta Aure danna nan

  • Falalar Yin Aure

    Falalar Yin Aure

    Aure shi ne ginshinƙin rayuwar mutane haɗi da yaɗuwar jinsin mutane, sannan  kuma dukkanin mutanan da basa yin aure ko gari ko jiha ko ƙasa za ka same su da  raunin tunani da hankali haɗi da rashin sanin ingantacciyar rayuwa. Aure yana da falaloli  masu girma ga waɗanda suka yi shi a matsayin sunnar ma’aiki (Sallallahu alaihi  wasallam) kuma suka kiyaye dokokin shi, ga kadan daga cikin su: 

    Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ya ce “Wanda ya yi aure, haƙiƙa ya  kammala rabin addininsa, to ya ji tsoron Allah a sauran rabin” Wato ibadar  da aka halicce ka don ka yi ta, idan ka yi aure, Allah SWT ya ba ka rabin ta kyauta.

    Mu’azu bn Jabalin (R.A)wani Sahabin Manzo (Sallallahu alaihi wasallam)  yace; “Sallar mai aure ta fi sallar marar aure sau arba’in”. Wato sai marar  aure ya yi sallah sau arba’in sannan za ya yi daidai da sallar mai aure guda ɗaya.

    Ibn Abbas (R.A) sahabin Annabi SAW, yace; “Ku yi aure, domin kwana guda  da aure shi ne mafi alheri daga ibadar shekara dubu”. Waɗannan hadisan  akwai su cikin Buguyatul Muslimina. Waɗanda ba su da aure, su yi ƙoƙari su yi  aure kafin duniyar ta tashi.

    Bukhari da Muslim su fitar da hadisi daga Ibn Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon  Allah s.a.w ya ce “Ya ku taron samari! Duk wanda ya sami iko daga cikinku;  to ya yi aure, domin shi ya fi taimakawa wajen rintse gani, kuma shi ya fi  taimakawa wajen kare farji. Wanda bai sami iko ba, to ya yi Azumi, domin  Azumi garkuwa ne”.

    Muslim ya fitar da wani hadisin daban daga Abu-Huraira (R.A) ya ce: Manzo  s.a.w ya ce “Idan ɗayanku ya ga wani abin da ya burge shi a jikin wata mace,  to ya koma zuwa ga iyalinsa, yin hakan zai mayar da abin da ke ransa na  sha’awa”. Waɗannan hadisai biyu sun nuna zahirin falalar da ke cikin aure da  kuma amfaninsa. Babbar falalar da ke cikin aure ita ce kare mutum daga  faɗawa cikin saɓon Allah ta hanyar kallon haramun ko aikata laifin zina.  Haka nan yana daga falalar yin aure akwai lada da Allah zai bai wa ma’aurata  a duk lokacin da suka biya buƙatarsu ta saduwa.

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) yana faɗa a cikin wani hadisi  cewa “A cikin tsokar ɗayarku (wato, saduwa) akwai ladan sadaka”, sai wani  Sahabi ya ce “Yanzu ɗayanmu ya biya sha’awarsa, sannan ya samu lada” sai  Manzon Allah s.a.w ya ce “Shin idan ya sanya ta a haramun zai samu zunubi? (wato idan ya yi zina)? Sai ya ce “Ƙwarai!” Sai Manzon Allah s.a.w “To haka  idan ya sanya ta a halal zai samu lada”.

    Na daga cikin falalar yin aure; samun ladan ciyarwa, Manzon Allah  (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce “Ciyarwar ɗayanku ga iyalinsa ladan  sadaka ne”. To kun ga waɗannan falaloli ba wanda zai samu sai wanda ya yi  aure. Don haka na ke jan hankali samari da ‘yan mata da a zage damtse wajen  yin aure domin riskar waɗannan falaloli.

    Ubangiji ka bai wa gwauraye cikin maza da mata damar yin aure. Ya kuma  sanya albarka cikin aurarrakin da aka yi da waɗanda za a yi. Ya Allah ka sa mu auri masu taƙawa da kwantar mana da hankali a duk lokacin da  muke cikin wani hali sannan su zamto hanyar shigarmu aljanna ameen. 

    Don karanta alamomin  shigar so danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake

    Yadda Alamomin Ciwon Sanyi Yake

    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi, kamar haka;

    • Ƙurajen gaba
    • Ƙaiƙayin gaba
    • Fitar da farin ruwa mai kauri
    • Jin zafi idan za a sadu
    • Jin zafi idan za a yi fitsari
    • Ɗaukewar sha’awa
    • Kunburin mara ko ciwon mara
    • Ƙanƙancewar azzakari ga namiji
    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin alamomin ciwon sanyi. Duk da yake fitar da farin ruwa a gaba yana daga cikin babbar alamar ciwon sanyi, amma shi kansa farin ruwa ba kowanne yake da matsala ba. Akwai mara matsala. Shi kansa farin ruwan da yake fita ya kai kala huɗu, ga su kamar haka;
    • Akwai mai fita fari tas, kamar koko mai kauri mara yauƙi ko kamar madara;
    • Akwai mai fita kamar gasara ko kuma in ce kamar kitse, wata ma sai ta sa hannu a ciki tana zaro shi;
    • Kuma akwai mai fitowa kamar zare a rinƙa zaro shi kamar zare, da ya taɓa jiki sai ya bushe;
    • Sannan akwai mai fita kamar majina mai haske mai ƙyalli mai yauƙi.
    Duk a cikinsu guda uku na ciwo ne wanda ba a sonsu a jikin mace. Wanda ake so shi ne mai fitar kamar majina, mai yauƙi, wannan shi ne ruwan ni’ima. Idan mace ta rasa shi a jikinta to akwai matsala. Samuwar ɗaya daga cikin ukun nan a jikin mace yakan hana wannan zuwa, daga nan sai ka ga mace ta shiga cikin damuwa. Domin karanta cikakken bayani akan Hanyar Warkar Da Ciwon Sanyi danna nan Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu

    Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu

    Akwai hanyoyi da yawa wajen rabuwa da irin waɗannan aljanu da ma wasu ba irin wannan ba. Ya zama duk inda aljani yake ajikin mutum sai ya gudu ya bar shi.

    Matakan Rabuwa Da Jinnu: Matakin farko akan so mara lafiya ta cire duk wani hoto a ɗakin da take kwana sannan ta kiyayi yawan kalle-kalle. Sannan ta sabarwa kanta kwanciya da alwala, idan za ta iya yi wa kanta ta yi da kanta, in kuma za ta sa ne a yi mata shi kenan, abinda dai ake so a yi shi yadda ya kamata. Duk lokacin da za ta kwanta bacci bayan ta yi alwala sai ta karanta waɗannan ayoyin kamar haka; 1. Aya ta ɗaya zuwa goma cikin suratul Kahf 2. Sai kuma ƙarshen suratul Mu’minun 3. Aya ta 54 zuwa ta 56 a cikin suratul A’araf Sannan ta karanta wannan addu’ar kamar haka;

    “Allahumma inni auzhubika min su’i ahlami, wa’astajiruka min talaubish shaidan fil yaƙzati wal manami”

    In kika karantata shi kenan sai ki yi baccinki. In Sha Allah muddin za ki kikayi wannan shawarar ba ki da matsala.

    Haɗin Turare

    Wannan turare aljani ba ya sonsa, duk inda ka turara aljani ba zai so wajenba In Sha Allah. Hannit Lubazzakar Habbatussaud Tafarnuwa Kajiji

    Waɗannan su ne za a haɗa su guri ɗaya sai a rinƙa turarawa. In kika yi haka ba ke ba aljanu In Sha Allah.

    Daddawar batso Habbatus sauda Kajiji Kustul hindi Al-mum Su ma turarawa za ayi da yardar Allah aljani zai bar jikin mutum da kuma gida. Sannan za a samu ruwa mai kyau, an fi son na zam-zam in ba a samu ba sai a yi amfani da ruwan rijiya ko kuma ruwan sama, ya zamo dai ruwan mai tsafta ne. Sai a yi alwala a nemi za’afaran mansa ko kuma garinsa sannan a samu ma’ul wardi sai kuma jan muski kaɗan sai kuma a samu ganyen magarya a niƙa shi a zuba kaɗan a ciki sannan a karanta wannan ayoyin kamar haka kowacce ƙafa bakwai ana yi ana tofawa cikin ruwa ko kuma numfashin na sauka cikin ruwan.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Suratul Fatiha Suratul Baƙarah aya ta 1-5 Suratul Baƙarah aya ta 101-102 Suratul Baƙarah aya ta 255-256 Ƙarshen Suratul Baƙarah aya ta 273-277 Suratul A’araf aya ta 54-56 Suratul Yunus aya ta 90-92 Suratul Isra’i aya ta 109-111 Suratul Mu’minun aya ta 113-118 Suratul Kahfi aya ta 1-10 Suratul Saffat aya ta 1-11 Suratul Mulk Suratul Jinn Suratul buruj aya ta 1-3 Suratul Kafirun Suratul Ikhlas Suratul Falaƙ Suratul Nas Waɗannan ayoyin su za a karanta a tofa a cikin ruwan sai a ba wa mara lafiya tasha da safe kafin ta ce komai, ta shafe kanta da ruwan kaɗan, sai kuma da daddare kafin ta kwanta bacci ya zama shi ne ƙarshen abin da za ta sha ta kuma shafe jikinta gaba ɗaya.

    Sannan waɗannan ayoyin za a karanta su kamar yadda suke, a samo mayuka kamar haka;

    Man habba Man kwakwa Man alayyadi Man zaitun Jan Muski (ɗan kaɗan) Man ridi A haɗe su wuri guda a karanta waɗannan ayoyin a tofa a ciki ta rinƙa shafawa a jikinta musamman in za ta kwanta bacci. Duk irin taurin kai da aljani yake da shi to zai bar jikinsa da yardar Allah. Domin karanta cikakken bayani akan Hanyar Ƙona Aljani Ajikin Mutum danna koren rubutu. Domin karanta bayani akan Addu’a A Lokacin Da Mutum Ya Fitinu Da Wasuwasi A Cikin Sallah danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Nau’ikan Sihiri

    a. Akwai kurciya

    b. Dan baka

    c. Sihirul firaƙ

    d. Sihirul muhabba

    e. Sihirul jini

    f. Sihirul tasrif

    g. Sihirul sariƙ

    Wannan su ne nau’i kaɗan daga cikin nau’ikan sihiri. Kowanne kuma da yadda ake yin sa. Ana yin sihiri mace ta saukar wa da ‘yar uwarta jini, ta rinƙa yin jini a duk lokacin da mijinta ke ɗakinta. Ana yin sihiri uba ya ji ya tsani ‘ya’yan wata sai na ɗaya. A na ma mutum sihiri ya ga duk abinda ya samu ya ruguje, ka ga kana samu amma kuma abun yana rushewa. Kuma ana iya yin sihiri a hana budurwa aure. Sannan ana iya yin sihiri mace ta rinƙa warin jaɓa, saurayi ya zo wajenta ya ji tana wari.

    Ana yi wa yaro sihiri dan a lalata rayuwarsa, ya zama ɓarawo, ɗan iska ko kuma ɗan shaye-shaye. Koma dai wane irin sihiri ne. Allah bai taɓa yin ciwo ba sai da maganinsa.

    Akwai matakai da ake bi domin a karya sihiri. Wani sihirin za a iya yi da an karya shi sai ya dawo, wani kuma da an karya shi yake tafiya. Sakamakon rashin kariya ne da tun farko ba a yi ba shi yasa da an karya zai iya dawowa.

    Da yawan waɗanda sihiri ke jikinsu ba su cika yadda da cewa sihirin ne ba. Gane sihiri aka yi maka, harka nemi maganin karya shi da na kariya shi ma arziki ne. Ga matakan da ya kamata ka ɗauka wajen maganin kariya yadda duk wani sihiri ba zai kamaka ba da kai da iyalanka, haka tsafin mai tsafi ba zai kamaka ba. Ko da mutum yana magana yana fitar da wuta a bakinsa saboda sihiri, to da yardar Allah ka fi ƙarfinsa. Sai dai a ganka ana faman duka amma ka kasa faɗuwa, ka zama shagwan mada. A kan yi amfani da ayoyi guda 33 a cikin Al-Ƙur’ani domin neman kariya daga sihiri.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Za ka karanta su ne bayan fatiha Suratul baƙarah aya ta 1-5 Ayatul kursiyyu aya ta 255 Amanar rasul zuwa ƙarshen surar Suratul A’araf aya ta 54-56

    Sannan ka karanta;

    “ƙulid’ullaha awid’ur rahman, ayyam ma tad’u falahul asma’ul husna, wala tajhar bi salatika wala tukhafit biha wabtagi baina zalika sabila”

    Har zuwa ƙarshen suratul Isra’i

    Da kuma suratus safat aya ta 1-11 Da suratur rahman aya ta 33-35

    Sannan ka karanta;

    “lau anzalna hazal ƙur’ani ala jabalin lara’aitahu khashi’an mutasaddi’an min khashyatillah, wa tilka amthalu nadribuha linnasi la’allahum yata fakkarun”

    Zuwa ƙarshen suratul hashri

    Da surar jinn aya ta 3-9 Sannan suratul buruj aya ta 20-22

    Waɗannan ayoyin akan samu ruwan rijiya ko na zam-zam ko ruwan sama a karanta su kowacce ƙafa bakwai a tofa a cikin ruwan, a sa za’afaran ko na mai, ko na gari, ko kuma na ciyawa. Sai a rinƙa ɗiba kaɗan ana sha da safe da kuma in za a kwanta. Za kuma a iya karanta su a tofa a cikin man zaitun da man habba da man kwa-kwa ko na riɗi, a rinƙa shafawa a jiki. Mutum zai iya shafawa da iyalansa gaba ɗaya. Muddin kai da iyalanka za ku rinƙa shafa wannan addu’ar, ba wani tsafin mai tsafi ko sihirin mai sihiri da zai yi tasiri a jikinka insha Allah. Sannan wannan addu’ar ka karanta ta a gidanka kullum da safe, Ubangiji zai ba iyalanka da gidanka kariya daga dukkan sharrin mutum da aljan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kariya Daga Hassada, Maita, Da Sharrin Aljanu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu