Tag: ilimi

  • Wasu Daga Fitattun Malamai A Ƙasar Sakkwato Da Kewayen Ta

    Wasu Daga Fitattun Malamai A Ƙasar Sakkwato Da Kewayen Ta

    Karatun Alƙur’ani a Sakkwato da kewayenta wanda ya haɗa da Gwandu da Gobir da Zamfara da Kebbi, ya sha bam-ban da karatun Alƙur’ani a masarautun Kanem-Barno.

    Haka kuma ya sha bam-ban da karatu a masarautun Kano da kewayenta wanda ya ƙunshi Haɗeja da Zazzau da sauransu don haka, magana a kan yanayin malaman Alƙur’ani a waɗannan larduna sun sha bam-ban.

    Makarantun Alƙur’ani a Barno da Kano da kewayen su sun fi ƙwarewa wajen haddace Alƙur’ani da naƙaltar logoginsa da shahara wajen rubuta shi da ka. Wannan ya sa ba sa kutsawa sauran fannonin ilmin Furu’a. A lardin Sakkwato da kewayen ta kuwa, koyo da koyar da Alƙur’ani ya fi ɗaukar salon ƙasashen Sudan da Mali da Mauritaniya, a inda ake haɗa Alƙur’ani da ilmi a cikin tsangaya.

    Kodayake yanayin karatun iri ɗaya ne da sauran sassan Arewacin Najeriya ta fuskar karatu da alluna da darasu, amma fa da almajiri ya yi saukar fari, to sai ya fara sauran fannonin Fiƙhu da Lugga da Hadisi da sauransu. Wannan yakan jawo taƙaituwar shagaltuwar makarantu wajen haddace Alƙur’ani. Don haka ma abu ne mai wuya zaƙulo tsantsar mahaddacin Alƙur’ani, ballantana wanda ke rubuta shi da ka a Sakkwato.

    A taƙaice dai kusan kowace makaranta Alƙur’ani a Sakkwato da kewaye za ka samu makaranta ce ko zaure ne na ilmi. Haka kuma duk wata cibiya ta ilmi, to akwai karatun Alƙur’ani a cikinta. Bugu da ƙari, babu cunkoson makaranta a wannan lardin kamar yadda abin ya ke a gabas kamar Maiduguri da Gaidam da Konduga da Potiskum da Paki da Haɗeja da makamantansu a yankin Kano da kewaye.

    Masarautar Sakkwato ta kafu daga baya-bayan nan in an danganta ta da Gobir da Zamfara da Kebbi.

    Shi kuwa rubutaccen tarihin yaɗuwar Addinin Musulunci a wannan yanki ya fi dangantuwa da ayyukan Shehu Usman da almajiransa. Tare da haka, tarihi ba zai manta da gudunmawar waɗanda suka fara kawo Musulunci wannan yanki ba, musamman ma ‘yan kasuwa Larabawa da gun-gun masanan nan da aka fi sani da “Malaman ‘Yan Doto”.

    Domin kuwa a wannan lokaci Gobir na daga cikin ƙasashen Hausa da suka fara karɓar baƙuncin malamai masana daga yammacin Sudan. Irin waɗannan malamai sun bar Malle tun cikin shekara ta 835AH (1431CE) a inda suka sauka a Gobir da Katsina; kafin ma su isa Kano.

    An ce Muhammad Korau (1445-1494), wan da ya kifar da sarautar Sarkin Katsina Kumayau; ne ya zama Sarkin Musulmi na farko a Katsina. Yana ɗaya daga irin wancan gungu na “Malaman ‘Yan Doto”; waɗanda suka yaɗa koyar da ilmin Alƙur’ani a lardin Sakkwato tun kafin bayyanar Shehu Usmanu.

    Karatun aIƙur’ani da ilmi ya samu wata irin bunƙasa da yaɗuwa a wannan lardi a lokacin da Shehu Usmanu ya bayyana. Almajirai da masana kowa na baje kolinsa don cin kasuwar ilimin gwarazan masana irin su; shi kansa Mujaddadi da ɗan uwansa Abdullahi da ‘ya’yansa irin su Muhammadu Bello da Nana Asma’u da almajiransu irin su; Abdullahi Alkanawi da wasu malamai irin su Wazirin Sakkwato Junaidu da Yahaya Alnawawi (alƙalin lardi) da Alƙali Abubakar Ladan Rame da sauran su. Don haka za mu nazarci rayuwar wasu daga irin malaman Alƙur’ani da na ilmi a wannan lardin; musamman ma daga ƙarni na ashirin.

    Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu)

    An haifi Malam Attahiru a farko-farkon sarautar Sarkin Musulmi Abubakar na Uku. Malam Attahiru ya taso cikin tarbiyyar addini wurin mahaifinsa. Kasancewar gidansu gida ne na ilmi da yaɗa shi; ya sa shi gadar wannan sana’a ta koyar da Alƙur’ani da ilmi.

    Duk da cewa a halin yanzu Malam Attahiru shi ne Limamin Masallacin Shehu da ke Sakkwato; duk da haka makarantarsa ba ta gushe ba ta na yaɗa addini a cikin garin Sakkwato tare da taimakon ‘yan’uwansa; musamman ma Malam Abubukar da Malam Ibrahim da Malam AbdurRahman da Malam Ahmad Zaruƙu.

    Malam Attahiru Na Liman tsatson AIƙali Abubakar Ladan Rame ne, wanda ɗan Gwaggon Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ne. Wannan zuriya mai albarka ta cigaba da jiɓintar koyar da addini da alƙalanci har zuwa kan Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu da ke Sakkwato na yanzu).

    Malam Buhari Siriddawa (Sarkin Malaman Sakkwato)

    An haifi Malam Buhari, Sarkin Malaman Sakkwato a Unguwar Siriddawa da ke Sakkwato a shekara ta 1934. Ya yi karatu wurin mahaifinsa Malam lbrahim da Malam Na Ta’ala Gidan Kanawa Sakkwato; da Malam Mujeli Garge da Malam Shehu NaLiman (Limamin Masallacin Shehu).

    A halin yanzu tsangayarsa cike ta ke da almajirai da makaranta sama da ɗari biyar; baya ga ɗumbin masu karatun littatafai kowace rana a wurinsa. Babbar baiwar Malam Buhari ita ce ƙwarewar da Ubangiji Maɗaukaki Ya ba shi a fagen ilmin Fiƙhu. A yanzu shi ne yake riƙe da ragamar jagorancin malaman Sakkwato a fadar Sarkin Musulmi. Makarantarsa na gudana ne tare da taimakon ɗansa Malam Sambo da wasu daga almajiransa.

    Malam Muhammadu Na Ta ‘ala

    Malam Muhammadu Na Ta’ala ɗaya ne daga zuriyar Sheikh Abdullahi Alkanawi, almajirin Shehu Usman kuma jakadansa. Asalinsa mutumin Kano ne daga jinsin Gyanawa. Ya koma Sakkwato a lokacin da ya samu labarin bayyanar Shehu. Daga nan kuma ya cigaba da taimaka masa a Sifawa. Bayan an dawo Sakkwato, Shehu ya ba shi fili inda ya gina gidansa da makarantarsa; wadda aka fi sani da Gidan Kanawa.

    Bayan rasuwarsa sai ɗansa Halliru ya zama halifansa Daga nan kuma sai ɗansa Umar; shi ma kuma ɗansa Ibrahim Dasuki ya gaje shi. Bayansa ne sai ɗan’uwansa Muhammad Na Ta’ala ya zama halifa.

    Wannan makaranta ba ta gushe ba ƙarƙashin ‘ya’yansa su Alhaji Bashir Muhammad Na Ta’ala; da ɗan’uwansa Malam Ahmad Zaruƙu, inda suke cigaba da ilmantarwa da wa’azi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Attahiru Shehu Na Liman (Limamin Masallacin Shehu) danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Zama A Madina

    Falalar Zama A Madina

    An karɓo daga Sa’ad (Radiyallahu anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: “Zaman Madina ya fi alkhari a gare su inda sun sani”, duk wanda ya bar Madina saboda ƙyamar ta; sai Allah ya kawo mata wanda ya fi shi.

    Duk wanda ya jurewa tsananin Madina da laulayinta zan cece shi kuma zan zama shaida a gare shi ranar ƙiyama.” (Muslim 1378.)

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Biyawa Wani Hajji Ko Umra danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Aikin Hajji A Sauƙaƙe danna nan,.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Tarihin Malam Mahmud Manzo Arzai

    Tarihin Malam Mahmud Manzo Arzai

    An haifi Malam Mahmud ɗan Muhammad ɗan Mahmud dan Muhammad a Damagaran cikin Jamhuriyar Nijar. Malam Mahmud ya zo Kano a lokacin girma ya fara kama shi. Malam Mahmud ya taso a hannun mahaifinsa a inda ya karanci Alƙurani.

    Ya shahara da sada zumunci da yawan kyautatawa ga baƙo da ɗan gari. Malam Mahmud ya yi tafiye-tafiye na neman Alƙur’ani izuwa alƙaryu masu nisa irinsu Inkibalwa da tsangayar Kolorum. Don haka ma ya sadu da manyan malamai irinsu Gwani Ahmad da Malam Yahaya da Alaramma Malam Yusuf wanda ake yi wa laƙabi da Malamin Mali da gwani Mahmud halifan Gwani Dipchan (shugaban makaratan Ƙasar Hausa) inda ya naƙalci ilmin Alƙur’ani da Rasmu da Tajwidi.

    Malam bai gushe ba yana kutsawa cikin neman Alƙur’ani da fannoninsa, har sai da ya sauka birnin Kano. A lokacin da ya iso kuwa almajirai suka riƙa dandazo don su sha daga tafkin ilminsa. Abu ne mai wahala ƙwarai da gaske ƙididdige yawan almajiran Malam Mahmud Manzo Arzai.

    Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Malam Muhamud Danja Zuwo, da Malam Lawan Saleh da Malam Gali Adhama.

    Wannan makaranta ta Malam Manzo ba ta gushe ba tana wanzuwa a hannun zuriyarsa cikc da ɗaruruwan almajirai, lokacin da Malam Manzo ya rasu babban ɗansa Malam Muhummad Mahmud wanda aka fi sani Malam Usman shi ya jagorance ta tare da taimakon ‘yan uwansa Malam Muktari Manzo mai koyar da ilimin Tajwidi da Malam Laminu shi ne mai darasu sai Malam Mustafa da Malam Abba da Malam Sunusi da Malam Ibrahim.

    Tsokaci

    Makarantar Malam Manzo Arzai ta shahara da ladabtar da kangarrarun yara ta hanyar addu’o’i da yi musu tarbiyya da karatun Alƙur’ani da lazimta musu addinin. A inda ake sanya su a mari. Mutane kan taso gari da gari don kawo ‘ya’yansu. Da yawa wannan tsari na tarbiyyantarwa ya kan taimaka wajen gyara tarbiyyar kangagararru har sai ka ga sun wayi garisun kintsu.

    Wasu ma sun zama malamai, albarkacin addu’o’i da lazimta musu Sallah akan lokaci da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Tarihin Sheikh Muhammad Barnoma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hutun Alhamis Da Juma’a A Tsangayu

    Hutun Alhamis Da Juma’a A Tsangayu

    Saboda irin himmar makaranta a tsarin tsangaya, alarammomi kan lazimtawa almajiransu yin karatu a wasu lokutan daban-daban bayan karatun safiya da maraice kamar haka:

    Tashe:-

    Akan tashi almajirai cikin dare jim kaɗan bayan fara barci da niyyar cigaba da kwami ko kuma tilawa. Wannan shi ne tashe ko jadare. Yanayin karatu a tsangaya kuwa kan ɗauki siffofi da dama musamman ma don ƙarfafa juna misali:-

    Musaffa:- Makarantan da suka tara tilawa kan haɗu a wasu lokuta musamman da dare su yi ta karatu a yanayin karɓa-karɓa ma’ana ana zagaya da’ira da tilawar sumuni-sumuni ko rubu’i-rubu’i. Da haka har a sauke ko kuma zuwa wurin da ya sauwaƙa. Da yawa makaranta kan kwana suna zuba tilawa a yanayi irin na musaffa ko tuƙuri.

    Ranakun Al’hamis da Juma’a su ne ranakun hutu a tsangaya. Wannan kuwa ya samo asali ne tun farkon Musulunci a lokacin da Sayyadina Umar ya yi tafiya ƙasar Sham kuma ya Jima Bai dawo ba. Wannan ya sa mutanen Madina cikin damuwa. Ko da labarin isowarsa ya iske su, sai kowa ya fito zuwa tarbo shi. Wannan ya sa yara ‘yan makarantar allo ba su yi karatu ba yini guda.

    A ranar Juma’a kuwa Amirul Muminina ya iso. Don haka aka ba su hutu kuma ya Zama hutun makarantunmu na Alƙur’ani.

    Domin karanta cikakken bayani akan Azuzuwa Da Kashe-Kashen Makaranta A Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ma’anar Tsangaya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Asalin Samuwar Goni

    Asalin Samuwar Goni

    Asalin kalmar Gwani/Goni kalmar Barbarci ce “Luhranni Gonni” ma’ana wanda ba ya kuskure in yana karanta Alƙur’ani.

    Kalmar Gwani dai-dai ta ke da Al’mahir da kalmar Al-Mukri, ma’ana ƙwararren makarancin Alƙur’ani. Kamar yadda mai irin wannan matsayi ake kiransa Fakih a Masar ko kuma Karmako a Senegal.

    Yaɗuwar amfani da matsayin Gwani tsakanin makaranta ya samo asali ne tsakanin ƙarni na goma sha zuwa ƙarni na goma sha tara a Maiduguri bisa sharaɗin makaranci ya sanya allo a gaban malaman Marte ko Gawala ko Konduga. To a nan ne za su ga can-cantar a naɗa makaranci a matsayin Gwani.

    A baya-bayan nan makaranci ba ya zama Gwani har sai ya sa allo gaban Goni Dala a Monguno ko kuma marigayi Goni Ƙashim cikin Maiduguri.

    Ga misalin ɗaya daga sarƙa ko silsilar naɗa Gwani tun kimanin sama da shekara ɗari huɗu da goma sha shida a Barno, wadda ta ke tuƙewa kan Goni Musa Dongol, farkon wanda aka fara kira Goni a tsohon birnin Ngazargamu. Wannan silsila ita ce “Daga Imam Mahir Sheikh Goni Isa ɗan Sayyid Adam wanda aka fi sani da Walda Am jileji daga Mahir Alwali Salih Goni Hamid Kidik daga Goni Bukar Konduga daga Mahaifinsa Goni Mustafa Yabe daga 120 Musa Afgalbiyama daga mahaifinsa Goni Nukabi Bardi daga mahaifinsa Goni Kadai daga Goni Mele daga Goni lbrahim Al’aysar daga Mahaifinsa Goni Umar Jundi daga Mahaifinsa Goni Musa Dongol”

    Tsokaci:

    Akwai saɓani a wasu lokutan wurin wasu malamai game da matsayin Gangaran. Shin wane ne gaba tsakaninsa da Gwani? Wannan ya biyo bayan wani shahararren makarin zance “gangaran ka fi gwani”. Ala ayyi halin Gwani shi ne mafi karɓuwar ajin ƙoli a azuzuwan makaranta, kamar yadda ya gabata. Amma fa a yanzu ba a ɗabbaƙa sharuɗan da a da sai makaranci ya cika su sannan ya samu matsayin Gwani.

    Shi kuwa Gangaran har yau sai wanda karatunsa ya bushe raƙayau sannan za a kira shi da wannan laƙabi. Ma’ana dai a yanzu in har ka ga wanda makaranta ke kira Gangaran to kusan za a iya cewa ya fi gwanin da aka naɗa ba tare da ya cika sharuɗan ba.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ɗabi’un Makaranta da Halayensu Cikin Zamantakewar Tsangaya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Kasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ƙalubale Ga Makarantun Tsangaya

    Ƙalubale Ga Makarantun Tsangaya

    Kamar yadda tarihi ke maimaituwa kullum, cikin kowane al’amari mai kyau ba ka rasa baragurbi ko zare. Tsarin tsangaya ma bai tsira ba.

    Tarihin musulunci da rayuwar sahabbai (Radiyallahu Anhuma) ya isa ishara, domin kuwa tun sahabbai (Radiyallahu Anhuma) ba su ƙare ba aka samu wasu mutane waɗanda ke da’awar Musulunci sun fito sun kishiyanci musulmi na ainahi. Irin waɗannan mutane sun haɗa da Khawarijawa da ‘yan Hururiyah da Murji’awa da Mu’utazilawa.

    Aƙidun waɗannan mutane sun ci karo kai tsaye da aƙidun musulmi. Don haka dukkan musulmin da yake son ya wanzu cikin musulmin ƙwarai dole ya kauce wa aƙidu da ta’adun waɗannan mutane da muka ambata.

    Makaranta cikin tsangaya su ma ba su kuɓuta daga irin waɗannan mutane da aƙidu ba. Da yawa mutane na kallon ma’abota tsangaya gaba ɗayansu a matsayin wani ɓangare na wani gungu na irin waɗansu jama’u da suka yi ƙaurin suna. Yin hakan rashin adalci ne ga nagartaccen tsarin mu na tsangaya.

    Za mu ɗauki irin waɗannan gungu na makaranta masu waɗannan aƙidu domin mu ƙara nazari:-

    1. ‘Yan Tatsine: Tatsine ko ‘yan Tatsine wasu mutane ne da ke da’awar su musulmi ne, masu karatun Alƙur’ani a yanayin irin na ma’abota tsangaya. ‘Yan tatsine sun samo asali ne ko sun ƙara fitowa fili a lokacin da wani mutum wai shi Muhammadu Marwa daga Marwa da ke ƙasar kamaru, ya tara gardawa masu neman karatun ƙur’ani ta hanyar sihiri da yaudara da yin da’awar annabtar ƙarya. Wanda daga ƙarshe ya haddasa rikicin da ya jawo asarar rayukan dubunnan mutane da dukiyoyi a birnin Kano.

    Dukkan wanda ya rayu a birnin Kano ko a Najeriya ta Arewa a dai-dai wannan lokaci to kuwa ya san irin barazanar da Tatsine ta haifarwa al’ummar jihar Kano. Wannan al’amari ya jawo har yau ɗin nan akwai ɓurɓushin irin waɗannan ‘yan Tatsine masu aƙidun ƙin yarda da komai na Hadisi ko Tafsirin Musulunci daga bakin magabata, idan ba bisa irin fassarar son ransu ba.

    In ba a manta ba gwamnatin wancan lokaci ta kafa wani kwamiti sakamakon wannan rikici na mai Tatsine a shekarar 1981 mai suna Kwamiti Kan Almajirai (Almajirai Committee 1987) ƙarƙashin jagorancin Malam Isa Waziri da Mambobi guda goma.

    Ayyukan wannan kwamiti sun haɗa da:-

    1. Duba yadda za a inganta tsarin karatun almajiranci duba ga abubuwan rashin daɗi da suka faru.
    2. Nazari kan dokokin da za su kula da zirga-zirgar almajirai da shawarwarin yadda za a ɗabbaƙa su.
    3. Aunawa da gano irin yadda tsarin almajirai ke haddasa gurɓatar ɗabi’un almajirai da sauransu.

    Bayan kammala aikin wannan kwamiti, gwamnatin Guruf Kyaftin Muhammad Ndatsu Umaru ta fitar da matsayarta game da shawarar kwamitin wadda suka haɗa da:-

    1. Yin doka kan zirga-zirgar almajirai.
    2. Yi wa makarantun Alƙur’ani Rajista ta hanyar mai Unguwa ko Dagaci ko Hakimi.
    3. Damar ƙwace izinin kafa makaranta ko zirga-zirgar malami da almajirai da sauransu.

    Wannan ya sa mutane da yawa har zuwa yau ɗin nan suna kallon tsarin tsangaya a matsayin wani tsari da ke da haɗari kuma suna kallon almajirai da gardawa ko ma alarammominsu a matsayin masu alaƙa da tatsinanci.

    2. ‘Yan Ƙala-Ƙato: Wannan wani reshe ne na tatsinanci wanda mafi yawan mabiyansa ma’abota tsangaya ne. ‘Yan ƙala-ƙato mutane ne masu son yin bayani game da ma’anonin Alƙur’ani; bisa son zuciya da rashin ilimin fannonin musulunci da harshen Larabci. Ma’abota tsangaya kan ruɗu da bin ‘yan ƙala ƙato da riƙe aƙidunsu saboda:-

    i- Rashin neman ilmin fiƙihu da sanin ilmin harshen larabci wanda sai da shi ne za a iya fahimtar saƙon Ubangiji maɗaukaki bisa sahihiyar ma’ana sanin kowa ne makaranta a tsarin tsangaya a arewacin najeriya suna da tawaya ta rashin neman ilmi fannonii fiƙihu don gyaran Sallah da fahimtar sauran mas’aloli.

    Da yawa za ka ga gardi wanda ya rubuta alƙur’ani bai san hukuncin ƙabil da ba’adi ba hakan takan sa; wasu makaranta na ganin idan mahaddaci ya shiga fagen neman ilmin karatunsa ba zai yi inganci ba. Wannan matsala game da makaranta a tsangayun arewacin Najeriya ta zama ruwan dare. Saɓanin tsangayu a ƙasahen Gambiya da Senegal da Mali da Sudan; waɗanda ke da ɓangare guda na ɗaukar ilimai da sauran fannoni kamar su; Ahlari da Ishimawi a Fiƙhu da Alfiyya da Kaɗarun Nada a Nahwu da Lamiyya a ilmin Sarfu da Jawahir a fannin Balaga.

    Wannan ya taimaka da gaske wajen samun mahaddata masu wayewa da gogewa a ilmi daban-daban a irin waɗannan ƙasashe ta yadda ba za a iya yaudararsu ko a ruɗe su ba.

    ii. Da yawan makaranta musamman gardawa sun fi nuna ƙwaɗayinsu; wajen neman laƙani da asiri don samun shuhura tsakanin abokan hamayya da kuma samun jama’a. Wannan ya sa duk wanda ke da wani abu irin wannan to kuwa za su sallama masa; kuma duk wanda zai yi musu tsawa a kan wannan ba kasafai suke samun jituwa da shi ba. Don haka da yawa suke son laƙani ko da kuwa zai kai su ga fita daga Musulunci.

    3. ‘Yan Magaru: ‘Yan Magaru wasu mutane ne da ake danganta su da ma’abota tsangaya. ‘Yan magaru sun shahara da tsafi da surkulle. Su ma aƙidunsu abin ƙyama ne kuma ba adalci ba ne a danganta duk wani matsafi da AIƙur’ani ba ko da kuwa ya haddace shi ko ya rubuta shi. A lokaci guda kuma ba adalci ba ne yi wa ma’abota tsangaya dukkaninsu kallon irin waɗannan mutane.

    Duba da irin manyan Gwanayen Alƙur’ani kuma gwaraza a fagen fannonin ilmi irin su Gwani Hamad da Shehu Rabi’u Ɗantinki da makamantansu. Waɗanda ke kwaɗaitar da mahaddata kan su tsunduma cikin fannonin ilmi. Babu shakka an yanke hanzarin duk wani ɗan tsangaya, sai dai in son zuciya ne ya halaka shi.

    Matashiya

    Akwai wata ta’ada da ta yi gurbi a zukatan ma’abota tsangaya masu yawa; irin wannan ta’ada shi ne rashin gwama karatu da sana’a ko kasuwanci. Da yawa ma wasu malamai kan ce “in ka ga mahaddaci na sana’a ai karatu bai albarka ba”. Don haka za ka ga mahaddata Alƙur’ani sun fi son su yi tsibbu.

    A wasu lokutan ma’ana kyarar su a wajen sauke Alƙur’ani a gidajen masu kuɗi. A gaskiya idan da makarantanmu za su yi ƙoƙarin koyi da magabata; da ba a bar su kullum a raɓe a soraye ana yi musu kallon raini ba. Alhali Ubangiji Maɗaukaki Ya ba su abin da bai ba wa kowa ba.

    Ya kamata a samu alarammomi Teloli da Kafintoci da Ma’auna da ‘Yan kasuwa da dai duk wata sana’a da ba za ta hana malam yin karatunsa ba. Labarin Malam Na Maiganji a Sashe Na Huɗu na wannan littafi ya ishe mu ishara.

    Domin karanta cikakken bayani akan Hanyoyin Farfaɗo Da Tsangayun Alƙur’ani danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Addu’ar Shiga Masallaci

    Addu’ar Shiga Masallaci

    “A’uzu bil-laahi aziimi, wabi wajhihil kariimi, wa sulɗaanihil ƙadiimi, minas-shaiɗaanir rajiimi. Bismil-laahi, was-salaatu was-salaamu alaa Rasuulil-laahi, Allaahummaftahlii abwaaba rahmatika”.

    {Ina neman tsarin Allah Mai girma, da na Fuskarsa mai Alfarma, da na Mulkinsa daɗaɗɗe, daga shaiɗan tsinanne. Da sunan Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam). Ya Allah! Ka buɗe mini ƙofofin rahamarka}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Fita Daga Masallaci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Nafilolin Sallah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Fita Daga Masallaci

    Addu’ar Fita Daga Masallaci

    “Bismil-laahi was-salaatu was-salaamu alaa Rasuulil-laahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), Allaahumma inni as’aluka min fadhlika, Allaahumma’asimnii minas-shaiɗaanir rajiimi”.

    {Da sunan Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya Allah! Ina roƙonka daga falalarka. Ya Allah! Ka kare ni daga shaiɗan tsinanne}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’o’in Kiran Sallah danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’a Idan Mutum Ya Yi Fushi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Ake Yi Bayan An Binne Mamaci

    Addu’ar Da Ake Yi Bayan An Binne Mamaci

    Annabi, (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance idan aka gama binne mamaci, sai ya ce; “Ku nema wa ɗan uwanku gafara, kuma ku roƙa masa tabbatuwa; domin yanzu ne ake yi masa tambayar ƙabari”.

    “Allaahummagfir lahu, Allahumma sabbit’hu”.

    {Ya Allah! Ka gafarta masa. Ya Allah! Ka ba shi tabbata}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Ziyarar Maƙabarta danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mene Ne Amfanin Zumunci? danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Yadda Ake Addu’ar Ziyarar Maƙabarta

    Yadda Ake Addu’ar Ziyarar Maƙabarta

    “Assalaamu alaikum ahlad diyyaari minal mu’uminniina wal muslimiina wa innaa in sha’allaahu bikum laa hiƙuuna. (Yarhamul laahul mustaƙdimiina minnaa wal musta’akhiriina) as’alul laaha lanaa wa lakumul aafiyata”.

    {Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma’abota waɗannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu ɗin Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji ƙan waɗanda suka yi saura. Ina roƙon Allah aminci daga bala’i, gare mu da gare ku}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Da Ake Yi Bayan An Binne Mamaci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Haƙƙin Wanda Mutuwa Ta Raba Shi Da Abokin Zamansa Daga Cikin Ma’aurata danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita; RMK