khairatu.shehu
Kalmar shaye-shaye, a ƙasar Hausa, musamman a Kano, ana alaƙanta ta ne da dafaffiyar albasa wadda ‘yan mata suke yin miyar romo suna sayarwa ga yara ƙanana, suna kiran sa da shaye-shaye da romo.
Har ila yau shaye-shaye yana nufin yin amfani da magunguna ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan zai iya haiffar da illa. Likitoci masu kula da lafiyar ƙwaƙwalwa sun bayyana cewa za a iya kiran mutum ɗan shaye-shaye matuƙar ya ƙi daina amfani da wani magani duk da sanin irin matsalolin ƙwaƙwalwa ko na jiki da wannan magani ke jawo masa.
Amma a wannan zamani da mutum ya ji an ce shaye- shaye abin da zai fara zuwar masa a zuciya shi ne shaye- shayen abubuwa masu sa maye, wanda a yanzu ya addabi jama’a, musamman matasa da iyayensu da hukumomi da kuma sauran jama’ar gari, tun da abin yana zama wata hanya ta kawo koma-bayan matasa ta kowace fuska alhali kuma matasan su ne ƙashin bayan ci gaban al’umma.
Don haka abin da ake nufi da shaye-shaye shi ne yin amfani da magani don wani dalili saɓanin wanda aka samar da maganin domin sa; ko kuma amfani da maganin da yake haramtacce ko kuma wanda ya saɓa da al’ada da tsarin zamantakewa. A taƙaice, ma iya cewa shaye-shaye na nufin kowanne ɗaya daga cikin waɗannan:
-Yin amfani da magani ba don inganta lafiya ba
-Yin amfani da magani don inganta lafiya, amma a sha fiye da yadda likitoci suka yi umarni
-Shan maganin da hukuma ta haramta
-Shan magani kowane iri ne ba tare da umarnin likita ba.
Domin karanta Menene Shan Ƙwaya? Danna nan
Edita@rumasau-kallamu