Raya Daren Lailatul Ƙadari

0
963

Daren Lailatul ƙadari, dare ne guda ɗaya da ake samunsa a watan Ramadan na kowacce shekara. Dare ne mai ɗimbin falala da daraja da babu wani dare da yake da irin waɗannan darajoji.

Allah Ta’ala ya saukar da sura guda akan bayanin darajar wannan dare wato suratul ƙadari. A cikin surar Allah ya bayana cewa wannan dare a cikinsa aka saukar da Alƙur’ani, kuma ya fi dare dubu wanda ya kama shekara tamanin da uku da wasu kwanaki ma’ana wanda ya dace da yin ibada a daren karɓaɓɓiya, za a ba shi ladan irin wannan ibadar na shekara 83.
Babu wanda ya san takamaiman daren nawa ga Ramadan ne daren Lailatul ƙadari, amma ingantattun hadisai sun tabbatar da cewa ana samun daren Lailatul ƙadari a dararen mara na goman ƙarshe na watan Ramadan, wato dararen 21, 23, 25, 27, da 29. Saboda haka, in goman karshe na Ramadan ya kama sai a ƙara zage dantse a ƙara kan Ibadun da ake yi domin neman dace.
Babu wata alama da ake gani da za a ce in mutum bai ganta ba, to bai yi dace da Lailatul ƙadariba. Amma a washe garin daren yanayi yakan kasance madaidaici.

Falalar Raya Daren Lailatul Ƙadari

An karɓo daga Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: wanda ya tsaya ya (raya) Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada, za a gafarata masa abinda ya gabata na zunubansa” (Bukhari 1082, Muslim 760).

labarin da ya wuceMuhimmacin Sanin Kamannin Annabi:
Labarin na GabaKyautata Tarbiyyar ‘Ya’ya