An haifi Husaini (Radiyallahu Anhu) ranar biyar ga watan Sha’aban Shekara ta huɗu da hijira, dai dai da Shekara ta 625 miladiyya, a Madina Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) shi ne ya sa masa suna Husaini, kamar yadda ya raɗawa yayansa Hasan, kuma shi ne ya yi masa haƙiƙa (ragon suna).
Hadisai da yawa sun tabbata kan falalar Husaini, ga kaɗan daga cikinsu:
1-An karɓo daga Bara’u ɗan Azib (Radiyallahu Anhu) yace: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ga Hasan da Husaini sai ya ce: “Ya Allah haƙiƙa ni ina son su, Allah ka so su (Ahmad da Tirmizi).
2-An karɓo daga Ya’ala Ibn Murrah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Husaini nawa ne, ni na Husaini ne, Allah yaso mai son Husaini, Husaini yana daga cikin jikokin annabawa” (Ahmad Tirmizi, Hakim).
3-An karɓo daga Aliyu Ibn Abi Talib (Radiyallahu Anhu) ya ce “Hasan ya fi kama da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wa Sallam) daga tsakanin ƙirjinsa zuwa kansa. Husaini kuma ya fi kama da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) daga ƙirjinsa zuwa ƙasa” (Tirmizi).
4-An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya Ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya Ce: “Hasan da Husaini su ne shugabannin samari ‘yan aljanna” (Ahmad Tirmizi, Hakim).
5-An karɓo daga Abdullahi Ibn Umar (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya faɗa kan Hasan da Hussaini cewa: “su ne abin jin ƙamshi na a duniya”. (Bukhari, Ahmad, Tirmizi).
6-Imam Husaini (Radiyallahu Anhu) mutum mai ɗimbin daraja ga yawan azumi da salla da sadaka da ayyukan alkairi mutum ne mai kwarjini da farin jini.
Husaini (Radiyallahu Anhu) ya yi shahada ranar juma’a goma ga watan muharram shekara ta sittin da ɗaya ga hijira a karbala.
Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Domin karanta cikakken bayani a kan Gaskiyar Abinda Ya Faru Na Shahadar Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.
Edita@rumasau-kallamu