Siffatuwar mumini da halataccen kishi, wata gudar alama ce da take nuna nagartarsa da kuma cikar ƙimarsa. Wannan ya sa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa maza da mata suka shahara da siffantuwa da halayyar kishi.
An karɓo hadisi daga Mugiratu ɗan Shu’uba (Radiyallahu An hu) ya ce:, Sa’adu ɗan Unada (Radiyallah An hu) ya ce: “(Ni kam) da zan ga wani mutum tare da matata, wallahi da na sare shi da kaifn takobina ba da faɗinsa ba.” Sai wannan magana da ya faɗa ta isa kunnen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Sai ya ce: “Kuna mamakin kishin Sa’adu ne? na rantse muku da Allah na fi shi kishi. Ni kuma Allah ya fi ni kishi….”. Muslim ne ya rawito shi.
Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce, “(wata rana) muna zaune wajen Manzon Allah t sira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya ce: “Wata rana ina bacci, sai na gan ni a Aljanna, kwatsam kuma sai ga ni ga wata mace tana yin alwala a gefen wani ƙerarren gida. Sai na ce “Wannan kuma na wane?” sai ya ce: “Na umar ne”. Sai na tuna kishin Umar, sai na juya na ba da baya. (Nan take) a wajen, sai Umar (Radiyallahu Anhu) ya fashe da kuka. Sannan ya ce: “Ya Manzon Allah yanzu kai zan yi wa kishi?” Bukhari ne ya rawaito shi.
Domin karanta cikakken bayani a kan Mene ne Maganin Ƙazamin Kishi(Haramtacce)? danna nan.
Wannan bayani an ciro Shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.