Wane Kishi ne Mafi Bayyana?

0
453

A duk kishin da bayi suke yi, babu mafi bayyana da fitowa sarari kamar iri biyu:

1. Kishin miji da mata, a tsakaninsu.
2. Kishi tsakanin kishiyoyi.

A bisa misali na farko, a baya mun ji cewa, sahabin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Sa’adu ɗan Ubada (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Da zai ga wani mutum tare da matarsa, sai ya sa kaifin takobinsa ya sare shi da ita”.
Sannan kuma an karɓo daga Abu Mulaika cewa, haƙiƙa A’isha (Radiyallahu Anha) ta ce: “Na rasa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wani dare (da yake da kwana a wajena), sai na zaci ko ya tafi wajen wata daga cikin matansa ne, sai na tafi bincike (da ban same shi ba), sai na dawo, kwatsam sai ga shi na gan shi ya yi ruku’u, ko sujjada yana cewa: “Subhaanaka wa bihamdika, la’ilaha illa anta”.  Sai na ce, “Mahaifina da mahaifiyata fansarka, kai kana cikin wani sha’ani. Ni kuma ina cikin wani sha’anin daban”. Nasa’i ne ya rawaito shi.
Don haka, idan ma’aurata na ƙwarai ne, ba sa barin ko-ta-kwana a duk lokacin da ɗayan su ya ga abokin zamansa yana aikata abin da zai sa Allah ya yi fushi da shi, ko kuma yana shirin aikata rashin gaskiya.
Dangane da misalin kishin da kishiyarta kuwa: Imamul Bukhari, Allah ya raham she shi ya rawaici hadisi da ke ɗauke da cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi saba, duk lokacin da ya yi sallar La’asar yana shiga wajen kowace ɗaya daga cikin matansa (don sanin halin da take ciki). To da yake Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mutum ne mai son kayan zaƙi da matarsa Zainab ‘yar Jahsh ta sami zuma, sai take ba shi ita ya sha; a duk lokacin da ya shiga wajenta. A dalilin haka, sai ya zama duk lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya je wajenta si ya daɗe fiye da yadda ya saba yi. Ganin haka, sai Nana A’isha da Hafsa suka shirya cewa, duk wadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya je wajenta daga cikin su, to, ta ce masa ya sha wani abu mai wari, domin kuwa wari yake yi. Da shigarsa kuwa wajen ɗayarsu, sai ta gaya masa haka, sai ya ce da ita, “Zuma na sha a wajen Zainab ‘yar Jahsh, amma tunda haka ne na rantse da Allah ba zan sake sha ba, amma fa kar ki gaya wa kowa dalilin haka”. Bayan haka sai Allah Ta’ala ya saukar da:

“Ya kai wannan Annabi mai ya sa kake hana kanka abin da Allah ya halatta maka domin neman yardar matanka. Allah mai matuƙar yafiya ne mai mayalwacin jinƙai ne.
Haƙiƙa Allah ya tilasta muku warware rantse-rantsenku (ta hanyar yin kaffara, wato horo da ya ɗora muku yin sa), kuma Allah ne majiɓincinku, kuma shi cikakken masani ne mai hikima, kuma a ya yin da Anabi ya asirta wani zance da wata daga cikin matansa, to, da ta ba da labarin zancen, kuma Allah ya bayyana masa shi, sai ya sanar da sashinsa ya kuma kau da kai daga wani sashe. To a lokacin da ya ba ta labari da shi, sai ya ce, masani wanda ya san komai ne ya ba ni labarin. Idan ku biyun kuka tuba zuwa ga Allah haƙiƙa da zukatanku sun karkata idan kuwa kuka tarar masa, to haƙiƙa Allah shi ne mataimakinsa da Jibrilu da muminai salihai, kuma mala’iku ma bayan haka mataimakansa ne”.
Sannan kuma, Imamun Nasa’I ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Anas da kuma Ummu-salama (matar Annabi) cewa, ita Ummu-salama ta kawo wa Annabi da sahabbansa abinci a mazubinta (a ranar kwanan Nana A’isha) sai ita kuwa A’isha ta tanƙwabi hannun tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi, sai mazubin ya faɗi ya dare gida biyu. Sai Annabi ya haɗa tsagi biyu na mazubin ya kuma tattara abincin a cikinsa, sannan ya riƙa cewa sahabbansa: “Ku ci babarku ta yi kishi, ku ci babarku ta yi kishi”. Sai sahabbai suka ci, Annabi kuma sai ya bar wannan fasasshen mazubin a wajensa har sai da A’isha ta zo da nata mazubin sai ya aika wa Ummu-Salama da shi. Sannan kuma ya ba  wa Nana A’isha fasasshen mazubin da ta fasa wa Ummu-Salama”.
Sannan kuma dai an karɓo hadisi daga Ummu-Salama cewa, sauran matan Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi maganar cewa, su fa ba su gane ba, mutane na kintatar ranar kwanan A’isha su aiko wa Annabi tsira da amincin Allah ya  tabbata a gare shi da kyauta, ai su ma suna son alheri kamar yadda A’isha take so. Da ranar Ummu-Salama ta zo kuwa; sai ta gaya wa Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi hakan. Sai Annabi ya yi shiru bai ce komai ba. Da ranar kwananta ta sake zagayo wa; sai ta sake yi masa wannan magana, sai ya kuma yi mata shiru bai ce da ita komai ba. Su kuma sauran matan sai suka tambaye ta cewa: Wace amsa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba ta? Sai ta ce da su, “Bai ce da ita komai ba”. Sai suka ce da ita, “to, kar dai ki ƙyale shi; har sai (ya magantu) ya ba ki amsa”. Da ranar kwananta ya kuma kewayowa, sai ta sake yi masa wannan maganar, sai Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: “Kada fa ku cutar da ni a game da A’isha. Duk cikin ku fa babu wacce aka taɓa yi mini wahayi a halin ina rufe da mayafinta in ban da A’isha”. Bukhari da Nasa’I ne suka rawaito shi.
Abin nufi da wannan amsa da Annabi tsira da amincin Allah  su tabbata a gare shi ya ba su; shi ne, idan har suna so su nuna kishinsu kan Nana A’isha, to su yi shi a kan abin da shi ya yi mata; ba a kan abin da wasu can daban suka yi mata ba, idan sun ce don me mutane suke yi masa abin alheri a ranar kwanan A’isha; to kuma mai za su ce game da wahayin da Allah ya yi masa a  lokacin yana lulluɓe da malulluɓin A’isha, amma kuma bai yi masa wahayi a yana lulluɓe da malulluɓin wata daga cikin su ba. Idan har ba su da ta cewa game da batun wahayin da Allah ya yi masa, to bai kamata kuwa su matsa masa a kan abin da sahabbansa suke yi masa a ranar kwanan A’ishan ba. Tun da dai ba shi ya ce da su idan za su yi masa abin alheri su keɓe ranar kwanan A’isha su yi masa ba. Wannan kenan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Mene ne Maganin Ƙazamin Kishi Haramtacce  Da Mene ne Matsayin Mumini Mai kishi ? danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceMene ne Matsayin Mumini Mai Kishi?
Labarin na GabaDuhun Kan Mace Mai Gaba da Kisihiya.