Matsalar Fata Dake ɓangaren Ido (CONJUNCTIVITIS)

0
170

Matsala ce dake faruwa ga ido, wani lokacin tana shafar ido ɗaya; wani lokaci kuwa za ta shafi idanuwan, idan har ido ɗaya ya fara, to ɗayan shi ma nan take zai harbi ɗaya.

Wannan ciwon ƙwayar viral infection ce ke kawo shi, wani lokacin kuwa “Bacterial infection”, ya danganta da yanayin ciwon.
Kuma ciwon kan bayyana a cikin kwana biyu zuwa mako uku (days-3wks).

ALAMOMI


Wani lokacin za a ga alamomin wannan ciwon kamar haka:
-Ƙaiƙayin ido
-Kumburin ido
-Canzawar ƙwayar idanuwa
-Zubar ruwa
-Rashin son hasken rana, kowane kalar haske na daban,
-Da sauran Alamomi.

Wannan ciwon conjunctivis a kan iya ɗaukar sa ta waɗannan hanyoyi kamar haka:
-Amfani da hankicif wanda mai wannan ciwon ke amfani da shi wurin shafe fuskarsa.
-Ko kuma gaisuwa idan mai wannan ciwon ya shafi idanuwansa.
-Da amfani da wasu hanyoyi marasa tsafta.

SHAWARA


-Tsaftace muhalli na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar ɗan Adam
-Hana yara zuwa makaranta idan sun kamu da wannan matsalar, domin gudun wasu su kamu
-Anfani da maganin antimicrobial na mai ko na ɗigawa
-Kawar da cutar ga yara musamman gonococcal_conjunctivitis
Idan kuwa abin ya yi tsanani, to sai a yi gaggawar zuwa asibiti domin ganin likita kai tsaye.

Domin karanta menene cutar Sikila danna koren rubutun

labarin da ya wuceIlimin Fisiyoloji (Physiology ) Cikin Harshen Hausa Kashi na Farko Masaitin jiki (Homeostasis)
Labarin na GabaCiwon Kumburi ɓangaren Mahaifar Mace (Pelvic Inflammation Disease (PID))