Magance Laulayin Da Magungunan Tazarar Haihuwa Suke Haddasawa

1
40

Na yi wannan rubutun ne saboda yawan ƙorafin da ‘yan-uwa mata suke yi a kan laulayin da magungunan tazarar haihuwa suke haifar musu. Magance laulayin ya danganta ne da irin maganin da mace ta yi amfani da shi da kuma nau’in laulayin. Kaɗan daga cikin laulayin da aka fi samu, da kuma hanyoyin magance su su ne:

  1. Magungunan tazarar haihuwa waɗanda ake yin su da sinadarai (hormonal methods): wannan ya ƙunshi dukkan magungunan tazarar haihuwa na ƙwayoyi (pills), allura (injections), na’urorin da ake sanyawa a ƙarƙashin fata (patches). Ana kiran su da magungunan tazarar haihuwa na sinadarai ne saboda ana yin su da sinadaran estrogen da progesterone. Laulayin da suke haddasawa su ne:
  • Tashin zuciya (nausea). Shan su tare da abinci yakan rage yiwuwar samun tashin zuciya. Ma’ana, a haɗa tare da abinci a lokacin da za a sha.
  • Ɓacin rai (mood swings); Idan mace ta shiga cikin yanayin ɓacin rai sakamakon amfani da magungunan tazarar haihuwa, to, sai ta koma asibiti domin a duba yiwuwar canza mata da wanda ba zai sanya ta ɓacin rai ba, ko kuma a canza mata adadin lokutan da ake sha (dosage change).
  • Rikicewar al’ada (irregular periods); Macen da ta sami wannan matsalar, ya kamata ta koma asibiti domin a duba yiwuwar canza mata maganin zuwa wanda yake da ƙarancin estrogen a cikinsa (low-dose estrogen), kamar Apri, Aviane, Yasmin, Levora, Ortho-Novum, da sauransu.
  • Ciwon nono (breast tenderness); Matan da suke shan ƙwayoyin combination pills masu ɗauke da estrogen da progesterone kamar Levofem, Yasmin, Alesse, Loestrin, da sauransu sukan fuskanci ciwon nono. Idan mace ta sami wannan laulayin, to, ta yi haƙuri domin zai bari da kansa. Idan bai bari ba, ko kuma ta damu, sai ta canza zuwa maganin only pill wanda ya ƙunshi sinadarin progesterone kaɗai, kamar norethindrone, Norgeston, Noriday, desogestrel, Cerazette, da sauransu.
  1. Hanyar tazarar haihuwa wacce ake sanya na’urori a cikin mahaifa (intrauterine devices – IUDs): na’urorin irin biyu ne. Akwai na copper mai suna “Mirena” kuma akwai na sinadari mai suna “Kyleena”. Laulayin da suke haddasawa su ne:
  • Ciwon mara ko ciki (cramping); Ana magance su ya hanyar yin amfani da magungunan kashe raɗaɗi na gama-gari (over the counter pain relievers), kamar ibuprofen, naproxen, diclofenac, aspirin, ketoprofen, acetaminophen, buscopan, paracetamol, da sauransu.
  • Rikicewar al’ada (irregular periods); Idan na’ura ce ta haifar da rikicewar al’ada, to, akwai buƙatar mace ta yi hakuri ta jira har na  ɗan lokaci mai tsawo, domin yakan daidaita kansa bayan watanni. Idan bai daidaita ba, to, ta koma asibiti domin a canza mata da wata na’urar.
  1. Hanyar tazarar haihuwa wacce ake amfani da makari (barrier methods); wannan ya ƙunshi hular mazakuta (condom), makarin mahaifa (diaphragm), hular bakin mahaifa (cervical cap), hular mazakuta mai sinadarin kashe ‘ya’yan maniyyi (spermicides condom), soson bakin mahaifa mai kashe ‘ya’yan maniyyi (cervical sponge), da sauransu. Laulayin da suke haddasawa su ne:
  • Bijirewar jiki (allergic reactions); Idan jikin mace ya bijire ma wani makarin da ta yi amfani da shi, to, canzawa zuwa ga wani makarin daban zai iya magance laulayin.
  • Cututtukan mafitsara (urinary tract infections); Idan aka yi amfani da makari wajen yin tazarar haihuwa, to, dole ne mace ta tabbatar da tsabtar gabanta, musamman idan ta yi fitsari, ko, kafin yin jima’i, ko bayan gama jima’i, ko lokacin da take yin al’ada. Hakan shi ne zai raba ta da laulayin yin amfani da makarai ɗin. Idan kuma ta kamu da cututtukan mafitsara, sai ta je asibiti domin a ɗora ta a kan maganinsu.
  1. Yanke bututun ƙwan haihuwa (sterilization); wannan hanyar yin tazarar haihuwa ce ta din-din-din, ma’ana har abada, domin idan aka yi wa mace tiyatar yanke bututun ƙwan haihuwa (fallopian tube), ba za a iya mayar da shi ba. Laulayin da yake haifarwa su ne:
  • Jin zafi a mara ko ciki bayan an yi tiyatar yanke bututun fallopian tube ɗin (post-operative pain); Za a iya magance shi ta hanyar yin amfani da magungunan kashe raɗaɗi (over-the-counter pain relievers).
  • Yin nadamar aikin tiyatar (post-operative regrets); Yawancin matan da suka je aka yi musu tiyatar yanke bututun fallopian tubes sukan yi nadama daga baya, domin mai yiwuwa ne su buƙaci haihuwa daga baya ɗin. Idan hakan ya faru, to, abinda kawai za a iya yi musu domin samun sauƙin damuwar shi ne maganganun kwantar da hankali (counseling).

Danna nan don karanta Lalurar Rashin Jin Ƙamshi Ko wari

Edita@rumasau-kallamu

 

labarin da ya wuceTarihin Sheikh Is’haƙ Rabi’u Khadimul Alƙur’ani
Labarin na GabaAllurar Da Ake Yi A Jijiya Da Allurar Da Ake Yi A Tsoka (INTRAVENOUS AND INTRAMUSCULAR INJECTION)

SHARHI ƊAYA