Laƙani Ta Hanyar Wuridi

0
492

Da yawan ‘yan tsibbu kan yi wani adadi mai yawa na wuridi. Wanda a mafi yawan lokuta sunayen aljannu ake kira.

Kuma koda an kira sunan Ubangiji Maɗaukaki, to kuwa za a sirka shi da waɗansu kalmomi ko haruffa da ba kasafai ake sanin ma’anarsu ba.

Za ka iya gane wannan nau’i na wuridi, ya yin da aka ce sai an nemo turare kaza, ko sai an samo garwashin wuta a cikin ɗaki mai duhu. Shi ma wannan yana da tasiri a fagen laƙunƙuna haramtattu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Alamomin Gane Malami Mai Sihiri Ko Matsafi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTsibbu Ta Hanyar Duba Ko Ilmin Taurari
Labarin na GabaAlamomin Gane Malami Mai Sihiri Ko Matsafi