Addinin musulunci addini ne da ya ƙunshi kowane sashe na rayuwa, addini ne da yake komai–da–ruwanka babu wani sashe na rayuwa komai ƙanƙantarsa da rashin muhimmancinsa a gurin mutane wanda bai yi magana akansa ba tunda dai har yadda mutum
Zai yi tsuguno sai da aka yi bayanin yadda za ayi shi a shari’ar Musulunci. Alqur’ani mai girma da hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da bayanan malamai na ƙwarai suna cike da waɗannan batutuwa.
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
Shari’ar musulunci itace kaɗai tsarin da zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ɗan adam. Tsari ne da ya wajaba duk wanda ya amsa sunan musulmi wanda ya yi Imani da Allah Ta’ala, da Manzancin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kasancewarsa cikamakin Annabawa da Manzanni, kuma ya yi imani da Alƙur’ani mai girma da kasancewarsa saƙon Allah Ta’ala na ƙarshe ga jinsin ɗan adam, duk wanda ya yarda da haka, ya zama wajibi akansa ya yi aiki da abinda Allah Ta’ala ya saukar (Shari’ar Musulinci) a kowane ɓangare na rayuwarsa gwargwadon ikonsa. Ba wai sai shugabanni kawai ba.
Shari’ar musulunci shari’a ce cikakkiya wacce ta shafe dukkanin shari’o’in annabawan da suka gabata, kuma itace sama da dukkanin wasu dokoki da tsare – tsare na ɗan adam, saboda ita tsarin mahaliccin ɗan adam ne wanda ya fi kowa saninsa. Duk wata doka da ta ci karo da ita, ta faɗi ta zama wofi ba ta da wata ƙima. Shari’ace mai sauƙi ƙwarai da gaske wacce ta dace da kowane lokaci da wuri da kuma kowaɗanne irin mutane.
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Shari’a ce da ba ta san kama–karya ko baba–kere ba, cike take da adalci da rahama da tausayi da bai wa kowa haƙƙinsa, sannan kuma tana tafiya daidai da zamani ba ta tsufa ballantana ta daina aiki. Wannan ne ya sa ba a taɓa kwaskware Alƙur’ani mai girma ko hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba, ko a ce za a yi musu wani gyaran fuska.
Yin watsi da shari’ar musulunci zunubi ne mai girman gaske wanda zai iya kai mutum ga kafirci. Yi la’akari da faɗin Allah Ta’ala: “Kuma duk wanda ba su yi hukunci da abinda Allah ya saukar ba waɗannan su ne azzalumai”. Da kuma faɗinsa Jalla jalallahu: “Kuma duk wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya sauƙar ba waɗannan sune fasiƙai”. (Ma’ida; 46)
Waɗannan ayoyi da waɗanda suka gaba ce su da waɗanda suke a bayansu da kuma ayoyi makamantansu da ɗimbin hadisai akan wannan batu suna nuna iri gagarumin hatsarin da masu ƙin aiki da shari’ar musulunci suke ciki. Duk ma wani tawili ko fassara da za a yi wa waɗannan ayoyi babu wata mafita ga masu bujurewa shari’ar Allah, saboda ko dai suka san ce kafirai masu bin tsarin kafirci ko azzalumai masu aikata zalunci ko fasiƙai masu aikin fasiƙanci.
Domin karanta bayani akan Jinya Da Likitancin Bahaushe Danna nan
Ko ma duka ukun Allah ya kiyaye mu Amin. Manyan–manyan dalilan da suka sa mafi yawancin musulmi suke yin watsi da shri’ar Allah sune;
- Rashin imani ko rauninsa.
- Neman yardar kafirai da gudun ɓata musu, da tsoronsu, da goya musu baya da kuma ruɗuwa da irin ƙyale–ƙyale da ci gaban mai haƙan rijiya da suke ciki.
- Jahiltar haƙiƙanin shari’ar musulunci, ta yadda za ka ga waɗansu shugabannin da ma mabiya sun kasance tantiran jahilai akan shari’ar musulunci. Waɗansu ma ko fatiha ba sa iya karantawa ballantana wani karatu na shari’a.
- Ruɗuwa da shuhubobi da ruɗani da maƙiya shari’ar musulunci suke tayarwa game da inganci da sahihancin shari’ar musulunci, irin wannan shuhubobi sun fi tasiri ga ‘yan boko da jahilan gari waɗanda suka ɗauki musulunci kamar wata al’ada ce kawai da ake haifar mutum a cikinta, amma ba shi da ruwa da harkokin rayuwa, wannan ba ƙaramin duhun kai ba ne da jahilci.
- Fakewa da zaman tarayya da baiwa waɗanda ba musulmi ba haƙƙoƙinsu, alhali Shari’ar musulunci ba ta tauye haƙƙin kowa, kuma su kafirai sai sun fi jin daɗi a tsarin shari’ar musulmi fiye da ko wanne irin tsari.
- Zargin shari’ar musulunci da cewa wai tsohon tsari ne wanda wai ya saɓawa yanayin rayuwar wannan zamani da wai aka ci gaba. Waɗannan ƙananan maganganu ba su kai matsayin zama dalili ba. Saboda haka ya wajaba ga dukkan musulmi ya yi fatali da su ya yi iyakacin ƙoƙarinsa wajen ganin tabbatar Shari’ar musulunci.
Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan
Haƙiƙa ƙin aiwatar da Shari’ar musulunci musamman a ɓangaren hukunci shi ne tushen dukkanin matsaloli da ci baya da rashin tsari da musibun da al’umar musulmi muke ciki a halin yanzu a ɓangarorin ita kan ta ibada, da aƙida, da zamantakewa da siyasa, da tattalin arziƙi da kuma tsaro.
Da ana aiwatar da Shari’ar musulunci tsantsa da mun rabu da miyagun aƙidu na zindiƙanci da ake ƙaƙaba su ga musulunci da mun yi ban kwana da bidi’o’i waɗanda suke mayar da mu daƙiƙai marasa wayewa, da mun yi sallama da irin wannan zaman ‘yan marina da muke yi zaman ‘ya’yan ɗinya, zaman harmagaza da rashin tsari. Da tuni mun mance da azzaluman shugabanni masu tsotse mana jini.
Masu cinye kai haɗe da hanci. Da kuma arziƙinmu ya bunƙasa kowa ya koma cikin hayyacinsa yana walwala da annashuwa sannan kuma da duniya ta yi lafiya, kowa ya samu aminci akan ransa da dukiyarsa da mutuncinsa da iyalansa da addininsa. Amma kash mun shiga cikin duhu, mun makance kuma mun runtuma wajen waɗanda suka fi mu makanta wai su muke so su yi mana jagora. Wannan ne ya sa kullum muke ƙara danna kai cikin rami muke yi.
Domin karanta bayani akan Mutuwa Da Rabon Gadon Bahaushe Danna nan
Ya Allah ka ganar da mu ka ba mu ikon bin tsarinka sau da ƙafa. Daga ƙarshe ya wajaba mu sani cewa wajibcin aiki da shari’ar musulunci bai tsaya akan Shugabanni kawai ba a a, aiki ne akan kowane musulmi ya bi dokokin Allah a aƙidarsa da ibadunsa da ma’amalolinsa na gida da kasuwa da wurin aiki da cinsa da shan sa da komai na rayuwarsa.
Su kuma Shugabanni su yi ƙoƙarin bunƙasa addininsu da tallafa masa da yaƙar munanan halaye da ɗabi’u da yin amfani da duk wata dama da suka samu wajen taimakon musulunci da musulmai da kuma kaucewa da bujirewa duk abinda ya saɓawa Shari’ar musulunci gwargwadon ikonsu. Ya Allah ka taimake mu ka sa mu dace Amin.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan