Hira, ko Kuma Shiga Ɗakin Wata Daga Cikin Matar Da ba Ranar Kwananta ba.

0
850

An karɓo hadisi daga A’isha (Radiyalahu An ha) ta ce, “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance babu wata rana face sai ya zagaya mu gaba ɗaya, sai ya yi kusa da wacce ya shiga wajenta ya shafa jikinta ba tare da ya biya buƙatar sha’awa da ita ba, har ya isa ga wacce take da kwanan ranar sai ya kwana a wajenta”. Imam Ahmad da Abu Dawud ne suka rawaito.

Bayan haka, cikin bayanan da suka gabata, mun ji cewa har zuma Manzo yake tsayawa sha in ya shiga wani ɗakin. Ashe nan halal ne miji ya zanta da matarsa ba a ranar kwananta ba, kamar yadda ya halatta gare shi ya shiga ɗakinta, ta ba shi wani abu ya ci, kuma ya sha.
Nawa Kwanakin Amarya, Kafin Daidaita Kwanakinta da na sauran matan da ta tarar?
An karɓo hadisi daga Anas (Radiyallahu An hu) ya ce: “Yana daga sunnar Manzon Allah tsira da amincina allah su tabbata a gare shi, idan magidanci ya auro budurwa zai kwana a wajenta sati guda, sai kuma ya yi rabon kwana; idan kuma ya auro bazawara zai kwana uku a wajenta, sai kuma ya yi rabon kwana”. Bukhari ne ya rawaito shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ke Sa Kishiyoyi Shiri Da Zaman Lafiya danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Duhun kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceShin ko ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗan tsubbu Domin Sihirce Kishiya?
Labarin na GabaMuhimman Abubuwan Da Suke Inganta Lafiya.