Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana

0
26

An karɓo daga Anas ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi sallar asuba a cikin jam’i, sannan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta ɓullo, sannan ya yi salla raka’a biyu za a ba shi ladan hajji da umra cikakku, cikakku, cikakku (Tirmizi 586). 

FALALAR LA ILAHA ILALLAHU 

An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: ” Wanda zai fi kowa azurta da samun ceto na ranar ƙiyama, shi ne wanda ya faɗi ” La ilaha illallahu” dan Allah (Bukhari: 99). 

An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “wanda ya ce: ” La’ilaha illalahu wahdahu laa sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’ in kadirun” sau ɗari (100) a yini guda, za a bashi ladan ‘yanta bayi goma, za a rubuta masa lada ɗari, za a shafe masa zunubai ɗari, zai sami kariya daga shiɗan a wannan yini har yamma, kuma babu wanda zai zo da wani abu da ya fi abinda ya zo da shi sai dai wanda ya aikata fiye da wannann.

Kuma wanda ya ce: ” Subhanallahi wa bi hamidihi” sau ɗari a yini guda, za a zubar da zunubansa koda yawansu ya kai kumfar teku. (Bukhari 3293, Muslim 2691).

Domin karanta Bayani akan Falalar Ba Da Sadaka Ga Ɗan Uwan Da Yake Gaba Da Kai Danna nan 

FALALAR TASBIHI 

Hadisai da yawa sun bayyana ɗimbin falala da darajar tasbihi. Ladan tasbihi da Alhamdulillahi yana cika tsakanin sama da ƙasa, tasbihi yana kankare zunubai, tasbihi yana daidai da yin kalmomi, ladan tasbihi ya fi duniya da abinda yake cikinta, tasbihi kalmomi ne da Allah yake matuƙar ƙaunarsu, da sauran darajoji masu tarin yawa.

An karɓo daga juwairiyya Haris (Radiyallahu Anha) ta ce: ” Wata rana Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fita daga wurinta bayan sallar asuba, ya bar ta a zaune a wurin da ta yi salla, daya dawo da hantsi ya tarar da ita tana nan dai a zaune, sai ya ce har yanzu kina nan a yadda na barki, ta ce na’am. 

Sai ya ce bayanki na faɗi waɗansu kalmomi huɗu da za a auna su da gaba ɗayan abinda kika faɗa yau sai su rainjaye su, sune: ” SUB HANALLAHI WA BIHAMDIHI, ADADA KHALƘIHI WA RIDA`A NAFSIHI WA ZINATA ARSHIHI WA MIDADA KALIMATIHI” (Muslim 2726). 

An karɓo daga Samarata Ibn Jundab (Radiyallahu Anhu) yace: ” Abubuwa haɗu su ne zancen da Allah ya fi so, za ka iya farawa da kowanne daga cikinsu: 

” SUBHANALLAH, WALHAMDU LILLAH, WA LA ILAHAILLALLAH, ALLAHU AKBAR” (Ibn Majah 3811). 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceFalalar Karatun Al- Kur’ani
Labarin na GabaRanar Haɗuwar Ango Da Amarya