Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:-
“Fazkuruunii azkurkum washkuruu lii walaa takfuruunii“
{ ku ambace ni, zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce min} (Baƙara, aya ta 152).
“Yaa ayyuhal – lazina amanuzkurul laaha zikran kasiiran wasabbihuuhu bukratan wa’asiilaa“.
{ Ya ku waɗanda suka yi Imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa } (Ahzab, aya ta 41).
“Wazzakiriinal – laaha kasiiran wazzaakiraati a’addallahu lahum magfiratan wa’ajran aziimaa“
{ Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma }
(Ahzab, aya ta 35).
“Wazkur Rabbaka fi nafsika tadharru’an wa khifatan wa duunal jahri minal ƙauli bil guduwwi wal’asaali walaa takun minal Gafiliina”.
{ Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai ƙasƙantar da kai da tsoro, ba da ɗaukaka murya ba (tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa), da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu } (A’araf, aya ta 205).
Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne”.
Kuma yace: { Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakar ku, kuma mafi ɗaukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku da ku haɗu da abokan gabarku ku riƙa dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Maɗaukaki}.
Kuma ya ce: { Allah Maɗaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin jama’a zan ambace shi a cikin jama’ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki ɗaya zan kusance shi kamu guda, in ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaɓa guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa }.
Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Shari’o’in Musulunci sun yi yawa a gare ni; saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riƙo da shi. Ya ce; { kar harshenka ya gushe face yana ɗanye daga ambaton Allah }.
Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce; { wanda ya karanta harafi ɗaya daga Littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki ɗaya saboda shi; kuma dukkan kyakkyawan aiki ɗaya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cewa Alif Lam Mim harafi ba ne a’a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne}.
Kuma daga Uƙbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai ya ce; A { wane ne daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ; ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba, ko yanke zumunta? } muka ce; “Muna son haka” .
Ya ce: { Ɗayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin Littafin Allah; Mabuwayi mai ɗaukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku; ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu, da kwatankwacin adadinsu na raƙuma }.
Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; {wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba; wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba; shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah}.
Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da suka zauna a wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba; kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya; in Allah ya so ya yi musu azaba, in ya so ya gafarta musu }.
Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da za su tashi daga wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki ne; kuma zai zamanto musu abin da- na- sani }.
Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’in Tashi Daga Barci danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.